TURKIYYA
2 minti karatu
Erdogan ya buƙaci ƙawayensu a NATO da su ɗage musu duk wani takunkumi na kasuwancin kayan tsaro
Shugaba Erdogan da takwaransa na Amurka Donald Trump za su gana a wani ɓangare na taron NATO da za a gudanar ranar Talata.
Erdogan ya buƙaci ƙawayensu a NATO da su ɗage musu duk wani takunkumi na kasuwancin kayan tsaro
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce yankin ba zia iya duakar wahalar yakin Isra'ila da Iran ba. / AA
24 Yuni 2025

Ya kamata kawaye a NATO su ɗage duk wani takunkumin kasuwancin kayan tsaro ba tare da wani sharaɗi ba, in ji Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, kafin tafiyarsa taron ƙungiyar tsaro ta NATO a birnin Hague.

Shugaban na Turkiyya ya kuma bayyana aniyar ƙasarsa ta karɓar baƙuncin taron ƙungiyar a 2026, inda ya bayyana aniyar Ankara ta samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, tare da bayyana ƙudirin samar da sabbin tsare-tsaren diflomasiyya bayan taron Istanbul.

Shugaba Erdogan ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tsakanin Iran da Isra'ila a baya bayan nan, amma ya yi kira ga manyan ƙasashen duniya da su yi gaggawar magance tashe-tashen hankulan.

"Yankin ba zai iya daukar nauyin yakin Isra'ila da Iran ba," Erdogan ya yi gargadi, yana mai kira ga dukkan bangarorin da su baiwa diflomasiyya dama ta gaske.

Erdogan ya kara da cewa: "Ba za a amince da matakan rashin hankali da Isra'ila ta dauka, tun daga Falasdinu har zuwa Lebanon, Siriya, Yemen da kuma Iran ba.”

Kazalika, Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya za ta ci gaba da yin tsaiwar daka kan matsayinta na kiyaye dokokin kasa da kasa da kuma bayar da fifiko kan harkokin diflomasiyya.

Erdogan ya kuma yi Allah wadai da kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta na dindindin a yankin Falasdin da kuma kai kayan agaji ba nan da nan.

"Ya kamata a aiwatar da tsagaita wuta mai ɗorewa a Gaza ba tare da bata lokaci ba, dole ne a dakatar da hare-haren Isra'ila kuma dole ne a bayar da damar kai kayan agajin jin kai cikin kwanciyar hankali zuwa yankin," in ji shi.

A wani yunkuri na karfafa hanyoyin diflomasiyya, Erdogan na shirin gana wa da takwaransa na Amurka, Donald Trump, a wani bangare na gefen taron da misalin karfe 2030 GMT, in ji mahukuntan Turkiyya.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us