TURKIYYA
3 minti karatu
Erdogan ya sha alwashin ba za a ƙyale masu nuna 'reni' ga Annabi Muhammad da sauran Annabawa ba
'Yan sanda sun kama wasu mutum huɗu a Istanbul saboda sa hannunsu a wallafa wani zanen barkwanci da ke 'nuna' Annabi Muhammad.
Erdogan ya sha alwashin ba za a ƙyale masu nuna 'reni' ga Annabi Muhammad da sauran Annabawa ba
"It is a clear provocation disguised as humour, a vile provocation," he railed, also denouncing it as a "hate crime". / AA
1 Yuli 2025

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa duk wanda ya nuna rashin girmamawa ga Annabi Muhammad (SAW) da sauran annabawa to za a gurfanar da shi a gaban doka.

“Za mu bi wannan al’amari,” in ji Erdogan a ranar Talata, bayan mujallar barkwanci ta Leman ta wallafa wani zanen barkwanci a fitowarta ta ranar 26 ga watan Yuni, wanda ke nuna rikicin Isra’ila da Iran, inda aka nuna cewa wai Annabi Muhammad da Annabi Musa suna gaisawa a kan wani birni da aka rusa.

“Wannan wata babbar fitina ce, wacce aka fake da sunan barkwanci,” in ji shugaban Turkiyya, yana mai jaddada cewa jami’an tsaro da na shari’a na kasar sun “dauki mataki nan take dangane da wannan laifin ƙiyayya,” inda aka ƙwace mujallar kuma aka fara aiwatar da matakan da suka dace.

Erdogan ya ƙara da cewa rashin girmamawa da wasu mutane “marasa tarbiyya da ladabi” suka nuna ga Annabi Muhammad (SAW) “abu ne da ba za a taba amincewa da shi ba.”

A cikin jawabinsa a wani taro tare da shugabannin jihohin Jam’iyyar AK mai mulki a Turkiyya, Erdogan ya yi kira ga matasa musamman, da su guji bari fushinsu ya rufe musu idanu.

Ya kara da cewa muddin suna kan mulki, “ba za su taba amincewa da wani ya zagi abubuwan da muke darajawa ba.”

Mutane hudu sun shiga hannun ‘yan sanda

A ranar Talata, an kama mutane hudu a Istanbul dangane da wallafa zanen barkwanci da ya nuna Annabi Muhammad (SAW).

Kamen ya biyo bayan binciken da masu gabatar da kara na Istanbul suka fara kai-tsaye dangane da laifin “zagin dabi’un addini a bainar jama’a.”

A shafin X, shugaban sashen sadarwa na Turkiyya, Fahrettin Altun, ya kuma yi Allah wadai da wallafar zanen, yana mai cewa Turkiyya “ba za ta ba wa wadannan mutane marasa kunya da ke kai hari ga dabi’unmu masu tsarki wata dama ba.”

“Wannan zagi da rashin girmamawa ga Annabinmu, jagoran Musulmai, ba za a iya ɓoye shi da sunan ‘yancin jarida ba,” in ji Altun, yana mai cewa an gurfanar da “wannan tunanin marar kyau” a gaban doka.

Ya kuma yi kira da a yi aiki da hankali.

A wani rubutu daban a X, Altun ya ce dukkan bangarorin gwamnati suna daukar matakan da suka dace “dangane da wannan mummunan hari kan imaninmu da dabi’unmu.”

“Yana da matukar muhimmanci ga ‘yan kasa su ci gaba da zaman lafiya kuma ka da su bari a tayar musu da hankali,” in ji shi, yana mai jaddada cewa suna bibiyar al’amarin “da azama.”

Duk wani abin da ba a so da zai iya faruwa a kusa da ginin mujallar ana hana shi “ta hanyar matakan da jami’an tsaronmu suka dauka,” in ji Altun.

A Musulunci, an haramta nuna hotunan annabawa. Wannan haramcin ya shafi Annabi Muhammad (SAW) da kuma Annabi Musa, wanda ake girmamawa a addinin Yahudanci da Kiristanci.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us