Mai ɗakin Shugaban Turkiyya, Emine Erdogan, ta yi bikin Ranar Iyalan Riƙo tare da isar da saƙo mai cike da tausayi a shafinta na X a hukumance, inda ta jaddada muhimmancin jin ƙai, da ɗaukan nauyi tare, da kuma daɗaɗɗiyar al’adar haɗin kan jama’a da ake da ita a Turkiyya.
“Duk lokacin da na haɗu da iyalan da suke rikon wasu yara, lamarin yana kawo mini farin ciki,” in ji Erdogan a ranar Litinin. “Ta hanyar irin misalinsu, muna ganin soyayya, da alheri, da jinƙai suna kai wa ƙololuwar daraja.”
A yayin bikin tare da iyalan da suk riko da yaran da suke kula da su, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta yaba wa jajircewar Turkiyya wajen kula da yara masu buƙatar taimako ta hanyar Tsarin Iyalan Riko.
“Mu al’umma ce da ke rungumar imanin cewa ‘mutane amana ne ga juna.’ Wannan al’adar haɗin kai tana ci gaba har zuwa yau ta hanyar Tsarin Iyalan Riko,” in ji ta.
Emine Erdogan ta kuma yi kira da a faɗaɗa tsarin iyalan riko har ya wuce iyakokin Turkiyya. “Ya kamata mu tuna cewa dukkan yara na duniya su ne yara ne da ake ƙauna na ‘ya’yan ɗan’dam,” kamar yadda ta jaddada.
Ta haskaka amincewar duniya ga aikin “Gönül Elçileri” (Masu Zuciya Mai Tausayi) ta Turkiyya, wanda aka gabatar a matsayin shirin abin kwatanci a hedikwatar UNICEF a birnin New York a bara. “Alfaharinmu ba zai misaltu ba kan halin tausayi na al’ummarmu da ƙasarmu ba,” in ji ta.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma miƙa saƙon taya murna ga matan gwamnonin Isparta, da Kahramanmaras, da Hatay—jihohi uku da aka yaba da ƙoƙarinsu na musamman a tsarin iyalan riko a wannan shekara—tare da yi wa dukkan yara da iyalansu fatan alheri.