Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tafi birnin Lachin na Azerbaijan don halartar bikin Ranar Samun ‘Yancin Kai ta Azerbaijan.
Ana sa ran Shugaba Erdogan zai gana da Shugaban Kasar Azerbaija Ilham Aliyev a ranar Laraba don tattauna alakar kasashensu da yin musayar ra’ayoyi kan al’amuran da ke wakana a yankinsu da ma duniya baki daya.
An kuma shirya shugaban zai halarci karo na biyu na taron ‘yan uku tsakanin Turkiyya, Azerbaijan da Pakistan wanda Firamnistan Pakistan Shehbaz Sharif ma zai halarta.
Ziyarar ta kuma hada da bikin kaddamar da Filin Jiragen Sama na Kasa da Kasa na Lachin da halartar bikin gargajiya na murnar Ranar Samun ‘Yancin Kai.
Babbar tawaga ce ta yi rakiya ga Erdogan, ciki har da ministoci da dama, da manyan masu bai wa Shugaban Ƙasa shawara da manyan jagororin jam’iyya mai mulki.