21 Yuni 2025
An samu fashewar wani abu a wani kamfanin ‘yan gwangwan a hanyar Mariri da ke babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutum biyar sakamakon fashewar inda mutum mutane da dama ke jinya a asibiti.
Gidan talabijin na Nijeriya ya ruwaito ‘yan sandan suna cewa lamarin ya faru a lokacin da wasu leburori ke sauke kayan gwangwan daga wata babbar mota da aka kawo daga Damaturu da ke Jihar Yobe.
Haka kuma tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Adamu Bakori wanda ya kai ziyara wurin ya bayar da umarni ga jami’an ‘yan sanda da suka ƙware wurin kwance bama-bamai su rufe wurin da lamarin ya faru domin guje wa ƙarin fashewar wani abu.