NIJERIYA
2 minti karatu
Ranar yara ta Nijeriya: Tinubu ya kaddamar da shirin dakile cin zarafin yara
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin ƙasar tana saka kuɗi kan wasu hanyoyin kare yara ciki har da manhajar kare yara (CPIMS) wadda ake ingantawa domin bibiya da kuma kai ɗauki kai-tsaye
Ranar yara ta Nijeriya: Tinubu ya kaddamar da shirin dakile cin zarafin yara
Shugaba Tinubu ya ce za kare yara daga cin zarafi / Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya
27 Mayu 2025

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da shirin daƙile duk wani nau’i na cin zarafin yara.

A saƙonsa ga yara na taya su murnar Ranar Yara ta Nijeriya wanda mai bai wa shugaban shawara na musamman kan watsa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya daƙile cin zarafin yara ba.

“Wannan shi ya sa nake ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a a faɗin ƙasa [mai taken] ‘[idan ka] ga wani abu, [ka] faɗi wani abu, [ka] yi wani abu’ a yau, inda [muke] ƙarfafa gwiwar ko wane ɗan Nijeriya ya zama gwarzon kare yara,” in ji shugaban .

Kazalika shugaban ya ce gwamnatin ƙasar tana saka kuɗi kan wasu hanyoyin kare yara ciki har da manhajar kare yara (CPIMS) wadda ake ingantawa domin bibiya da kuma kai ɗauki kai-tsaye

“Ya ‘yan’uwana ‘yan Nijeriya da kuma ‘ya’yanmu, mun ba da fifiko wajen kare yara a ƙarƙashin shirin Ajandar Sabunta Fata. Wannan ya haɗa da ɗabbaka Shirin kawo ƙarshen cin zarafin yara (na shekarar 2024–2030), wanda na ƙaddamar kwanan nan,” in ji shugaban.

 Ya ce shirin ya tsara cikakken jadawalin yadda za a hana cin zarafin yara da hukunta masu cutar da yara tare da tallafa wa waɗanda aka ci zarafinsu.

Cin zarafi na ɗaya daga cikin matsalolin da yara suke fuskanta a Nijeriya duk da ƙoƙarin da hukumomi ke yi na kare yaran.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us