NIJERIYA
2 minti karatu
APC da PDP na gudanar da tarukansu na Majalisar Ƙoli a Abuja
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027 a Nijeriya, ana sa ran taron da APC za ta gudanar a fadar shugaban ƙasa da wanda PDP ke gudanarwa a Wadata Plaza za su yi tasiri ga babban zaɓen ƙasar da ke tafe.
APC da PDP na gudanar da tarukansu na Majalisar Ƙoli a Abuja
Wadannan tarurruka na NEC suna da matuƙar muhimmanci ga makomar manyan jam’iyyun nan biyu kafin zaɓen 2027. / Others
24 Yuli 2025

Manyan jam’iyyun siyasa guda biyu na Nijeriya, APC da PDP, na gudanar da tarurrukan majalisar ƙoli (NEC), inda Jam’iyyar PDP ta fara nata taron tun a ranar Laraba ita kuma APC za ta gudanar a ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne a yayin da suke ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryensu na babban zaɓen shekarar 2027.

Jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) ta sauya wurin taronta daga hedikwatar jam’iyyar da ke Wuse II, Abuja, zuwa Dakin Taro na  Fadar Shugaban Ƙasa. Za a fara taron da misalin ƙarfe 2:00 na rana.

A jiya Laraba Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnoni 22 na jam’iyyar APC ƙarkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma, inda suka tattauna kan matsalolin cikin gida gabanin gudanar da taron majalisar ƙoli na jam’iyyar a ranar Alhamis.

Ana sa ran taron zai tattauna batutuwa kamar naɗin sabon shugaban jam’iyya na ƙasa wanda zai maye gurbin Dakta Umar Ganduje da batun ware muƙamai na shiyya-shiyya (zoning) da tsarin rajista ta yanar gizo da sauye-sauyen cikin gida.

PDP ta fara taronta a ranar Laraba

Jam’iyyar adawa ta PDP ta fara gudanar da taronta na majalisar ƙoli na 101 a ranar Laraba a hedikwatarta da ke Wadata Plaza, Abuja. Taron ya fara da misalin ƙarfe 2:00 na rana kuma zai ci gaba har zuwa Juma’a, 25 ga Yuli.

A cewar Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyya, Debo Ologunagba, za a tattauna batun sulhu da gyaran jam’iyya, da kuma yadda za a tsara babban taron jam’iyya na ƙasa (convention). Ana kuma sa ran za a tabbatar da sabbin shugabannin jam’iyya da za su jagoranci shirye-shiryen zaɓen 2027.

Ana sa ran mahalarta taron su haɗa da shugaban jam’iyya na ƙasa, tsofaffin shugabannin ƙasa waɗanda har yanzu suke cikin jam’iyyar da mataimakansu da gwamnoni, mambobin kwamitin amintattu (BoT), da ‘yan majalisar tarayya.

Muhimmancin Taron Ga Zaɓen 2027

Wadannan tarurruka na NEC suna da matuƙar muhimmanci ga makomar manyan jam’iyyun nan biyu kafin zaɓen 2027.

Ga APC, an sa ran za a warware rikicin shugabanci da kuma tattauna yadda za a rarraba mukamai bisa yankuna. Ga PDP kuwa, taron zai taimaka wajen warware matsalolin cikin gida da ƙarfafa shugabancin jam’iyya.

Sakamakon waɗannan tarurruka zai nuna shirin kowace jam’iyya da ƙarfin ta wajen shiga fafatawar siyasa a 2027.

 

 

 

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us