WASANNI
2 minti karatu
India ta ƙi amincewa da Xavi Hernandez ya zama kocin tawagar kwallon kafa ta kasar
Tsohon kocin Barcelona, Xavi Hernandez ya gaza samun damar horar da tawagar ƙwallon ƙafa ta India, bayan an ƙi amincewa da neman da ya yi a rubuce.
India ta ƙi amincewa da Xavi Hernandez ya zama kocin tawagar kwallon kafa ta kasar
Andres Iniesta Tattarwar Yada Labari - An'gani Ci Gaba / Reuters
25 Yuli 2025

Hukumar ƙwallon ƙafa ta India (AIFF) ta yi watsa da buƙatar neman horar da tawagar ƙwallo ta ƙasar daga tsohon kocin Barcelona, Xavi Hernandez.

Duk da cewa Xavi ya samu shiga jerin waɗanda ke kangaba wajen damar zama kocin India, kwamiticin ƙwararru na hukumar ƙwallon bai amince da neman nasa ba.

Babban dalilin da suka ce ya hana, shi ne girman kuɗaɗen da za a kashe wajen ɗauko koci mai daraja irin ta Xavi, wanda babban koci ne ɗan Sifaniya.

Baya ga Xavi, hukumar ta samu jerin masu neman aikin horar da tawagar India, ciki har da wasu tsaffin ‘yan wasan Liverpool, Robbie Fowler da Harry Kewell.

Haka kuma, akwai wasu kociyoyin da suka saba aiki a babbar gasar ƙwallo ta ƙasar, wato Indian Super League, kamar su Kibu Vicuna, Eelco Schattorie, da Khalid Jamil.

Xavi na neman aiki

Adadin waɗanda suka gabatar da neman zama kocin India ya kai 170 daga sanannu zuwa ƙananan koci-koci daga faɗin duniya.

Sai dai duk da India ta ƙi amincewa da bai wa Xavi Hernandez aikin, masana ƙwallo na kallo harkar ƙwallon ƙafa a India tana samun tagomashi, ganin yadda har irinsu Xavi sun fara shigar ta.

Shi dai Xavi ba shi da ƙungiyar da yake jagoranta a halin yanzu bayan da ya bar horar da Barcelona a 2024. Ya ciyo wa Barca kofin La Liga na kakar 2022–23.

Gabanin zama koci, Xavi Hernandez tauraron Barca ne, wadda ya buga wa wasanni sama da 700 kafin ya yi ritaya. Kafin nan ya horar da Al Sadd ta Qatar inda ya lashe kofin kasar da su.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us