An gudanar da jana’izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ranar Talata a gidansa da ke birnin Daura na Jihar Katsina a arewacin ƙasar.
An binne gawar marigayi Muhammadu Buhari ne da misalin karfe shida na yamma a agogon Nijeriya bayan kai ta Daura daga filin jirgin saman birnin Katsina.
An yin masa sallah sannan daga bisani aka yi masa jana’izar ban-girma ta soji.
Buhari ya rasu ne a birnin Landan ranar Lahadi yana da shekaru 82 a duniya.
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar a karkashin sanya idon shugaban Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.
Wasu daga cikin manyan mutanen da suka halarci jama’izar sun hada da shugaban kasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo; firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zaine da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da hamshakin dan kasuwar Afirka Aliko Dangote.