TURKIYYA
3 minti karatu
Babban jami’in diflomasiyyar Birtaniya ya yaba da rawar da Turkiyya ke takawa a zaman lafiyar yanki
Sakataren harkokin wajen ya yi bayani game da haɗin gwiwa da cinikayya da kuma tarayya a harkokin diflomasiyya a lokacin ziyararsa a Ankara.
Babban jami’in diflomasiyyar Birtaniya ya yaba da rawar da Turkiyya ke takawa a zaman lafiyar yanki
Ministan harkokin wajen Turkiyya Fidan da sakataren harkokin wajen Birtaniya Lammy sun yi taron manema labarai bayan ganawarsu a Ankara, Turkiyya. / AA
1 Yuli 2025

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya yaba da irin muhimmiyar rawar da Turkiyya ke takawa a yanki yayin wani taron manema labarai a Ankara bayan ganawa da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan. 

Ranar Litinin Lammy ya jaddada muhimmancin dangantakar diflomasiyyar da ke tsakanin Birtaniya da Turkiyya, wadda aka gina ta bisa tattaunawa a-kai-a-kai da haɗaka na dabara da kuma alaƙa mai zurfi ta al’ada

"Cikin watanni 12 [da na yi] a aiki, babu wani watan da ya zo da ban gana ko yi magana, yawanci sama da sau ɗaya, da minista Hakan Fidan ba," in ji shi, yana mai bayyana ƙarfi da yawan lokaci na tattaunawa tsakanin Birtaniya da Turkiyya.

Lammy ya yi ishara da kimanin ‘yan Birtaniya miliyan biyar da ake kiyasin cewa za su ziyarci Turkiyya bana da kuma kasancewa al’ummomi masu amfani da harshen Turkanci a Birtaniya a matsayin hujja ta alaƙa tsakanin mutanen ƙasashen biyu. 

Ya jaddada muhimmancin tattaunawar da ake yi na yarjejeniyar cinikayya ba tare da haraji ba wanda za a gina a kan cinikayyar da ta kai fam biliyan 28 (dala biliyan 38.4) a ko wace shekara. 

“Kasancewa masana’antu da ‘yan kasuwan Turkiyya suna aiki tare da, a mafi yawan lokuta a cikin Birtaniya, wata alama ce ta wannan ƙwaƙƙarar dangantakar,” in ji shi.

Rawar da Turkiyya ke takawa a Yukrain da Gaza da Syria

Lammy ya yaba da rawar da Turkiyya ke takawa wajen shiga tsakani domin samar da zaman lafiya da kuma mayar martani ga harin tsokanar Rasha a Yukrain, yana mai tuna aikin da Ankara ta yi wajen samar da kwanciyar hankali a Bahar Aswad da kuma biɗar tsagaita wutar da aka daɗe ana nema.

“Ina godiya sosai ga aikin da Turkiyya ta yi wajen neman samar da zaman lafiya da kuma kawo ƙarshen rasa rayuka da yawa da ake,” in ji shi, yana mai ishara ga yadda ake rasa rayukan fararen hula ‘yan Yukrain da sojojin Rasha.

Game da Gaza, Lammy ya jaddada damuwar ƙasashen biyu kan lamarin na jinƙai kuma ya jaddada goyon bayan mafita ta ƙasashe biyu. Ya kuma tabbatar da cewa Syria batu ne da ake tattaunawa a kansa, yana mai tabbatar da godiyar Birtaniya ga haɗin kan Turkiyya kan lamuran tsaron yanki.

“Muna da dangantaka ta kut-da-kut a ɓangaren aiki, kuma ina ganin za ku ga ƙarin haɗaka na aiki cikin watannin da ke zuwa tsakanin Birtaniya da Turkiyya a wannan lokacin mai matuƙar wahala da ƙalubale a siyasar duniya,” in shi.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us