WASANNI
1 minti karatu
Liverpool ta cim ma yarjejeniyar £116m kan Wirtz
Wannan yarjejeniyar za ta kasance yarjejeniya da ta fi tsada a tarihin Liverpool.
Liverpool ta cim ma yarjejeniyar £116m kan Wirtz
Idan aka kai ga biyan dukkan kuɗaɗen yarjejeniyar, ɗan wasan zai fi kowa tsada a tarihin ƙwallon ƙafar Birtaniya / Reuters
13 Yuni 2025

Zakarar Gasar Firimiya ta bana Liverpool ta cim ma yarjejeniyar fam miliyan 116 domin siyan ɗan wasan Jamus Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen.

Yarjejeniyar da aka cim ma kan ɗan wasan mai shekara 22 na da fam miliyan 100 a matsayin garanti da kuma fam miliyan 16 da za a ƙara.

Za a iya biya ƙarin kuɗin ne idan ƙungiyar ta samu nasarori a jere, lamarin da zai sa ɗan wasna ya kafa tarihi a Birtaniya.

Har kawo yanzu dai yarjejeniyar da ta fi tsada a karon farko a tarihin Birtaniya ita ce yarjejeniyar fam miliyan 107 da Chelase ta yi kan ɗan wasan Ajentina Enzo Fernandez daga Benfica a shekarar 2023.

Chelsea ta kuma sayi ɗan wasan Brighton kan kuɗi fam miliyan 100, wanda zai iya kaiwa fam miliyan 115.

Sai dai kuma wannan yarjejeniyar za ta kasance yarjejeniya da ta fi tsada a tarihin Liverpool.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us