NIJERIYA
2 minti karatu
EFCC ta kama fitacciyar ‘yar TikTok Murja Kunya kan zarginta da wulakanta Naira a Nijeriya
A sanarwar da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin, ta ce an kama Murja ne saboda zarginta da liƙa kuɗin Naira don nishaɗi a yayin zamanta a otel ɗin Tahir Guest Palace a Kano.
EFCC ta kama fitacciyar ‘yar TikTok Murja Kunya kan zarginta da wulakanta Naira a Nijeriya
A watan Janairun 2025 ne aka fara kama Murja saboda take dokar CBN, wadda ta haramta wulaƙanta naira. / Others
17 Maris 2025

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Nijeriya Zagon Ƙasa ta kama fitacciyar ‘yar TikTok Murja Kunya kan zarginta da wulaƙanta kuɗin Naira.

A sanarwar da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin, ta ce an kama Murja ne saboda zarginta da liƙa kuɗin Naira don nishaɗi a yayin zamanta a otel ɗin Tahir Guest Palace a Kano.

“Kamen nata ya biyo bayan bibiyar da jami’an EFCC suka dinga yi mata ne bayan da ta tsere daga belin da hukumar ta bayar da ita kimanin wata guda da ya wuce,” in ji EFCC.

A watan Janairun 2025 ne aka fara kama ta saboda take dokar Babban Bankin Nijeriya CBN, wadda ta haramta wulaƙanta naira.

EFCC ta ce ta ba da belinta har zuwa lokacin da za a gabatar da ita a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano. Amma da lokacin gurfanar da ita a gaban kotu ya yi, sai ta gudu don kauce wa shari’a.

Sai dai hukumar ta ce bayan da aka shafe makonni ana bincike, sai jami’anta suka yi nasarar sake kama ‘yar TikTok din ranar Lahadi 16 ga watan Maris din 2025, inda aka miƙa ta ga reshen hukumar da ke jihar Kano, inda a yanzu take jiran shari’a.

EFCC ta jaddada aniyarta ta tabbatar da dokoki da kare darajar kuɗin Nijeriya, tare da yin gargaɗi kan duk masu wulaƙanta naira ta hanyar yin liƙi da taka ta a lokutan bukukuwa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us