Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya yi gargaɗin cewa cigaba kisan ƙare-dangi a Gaza da rikici da Iran zai iya shafar yankin, da Turai da Asiya "tsawon shekaru".
Cikin gaggawa yaƙin Iran da Isra’ila yana kai wa "matsayi da ba za a iya shawo kansu ba", yayin da gwamnatin Amurka ke auna yiwuwar shiga yaƙin.
“Abin takaici, kisan kiyashi a Gaza da yaki da Iran suna neman kai wa wani matsayi da ba za a iya shawo kansu ba. Dole ne a kawo ƙarshen wannan dabbancin ba tare da bata lokaci ba,” in ji Erdogan.
Ya ce, "Yana da alfanu a ɗauke hannaye daga kan makamai kafin a samu ƙaruwar ta’adi, zubar da jini, da kisan farar-hula a wannan mummunar rikici. wanda zai iya illata yankinmu, da ma Turai da Asiya tsawon shekaru”.
Erdogan ya ɗora alhaki kan gwamnatin Netanyahu na “kisan kiyashin” da ke faruwa a Gaza, kuma ya zargi wadanda ke ci gaba da yin gum duk da kisan da ke faruwa, yana cewa suna da hannu.
Ya ce, “Waɗanda ke mayar da Gaza mafi girman kurkuku amma kuma suna kukan ana aikata laifukan yaki to ba su da adalci, amma suna nuna rashin kunya da karfin-hali”.
Ya kuma yi kira ga manyan ƙasashen duniya da ke da faɗa-a-ji kan Isra’ila su guji daɗawa “yaudara Netanyahu” sanna maimakon haka su yi amfani da ƙarfinsu don ɗabbaƙa tsagaita wuta da maido da lumana a yankin.
Erdogan ya ce, “Duk da barazanar ‘yan korar Zionist da kuma masu gaba da ni da gwamnatina, ba mu taɓa raurawa kan matsayarmu ba kuma ba mu taɓa shakkar kare waɗanda aka zalunta ba”.
Kwararar baƙi, barazanar zurarar nukiliya
Shugaba Erdogan ya yi kalaman ne yayin taron matasa na Kungiyar Hadin-kan Musulmi ta (OIC) a Istanbul, gabanin taron ministocin OIC a ƙarshen mako.
Cikin waɗanda za su halarci taro akwai ministan wajen Iran, Abbas Araghchi, kuma rikcinsun da Isra’ila zai zo kangaba a ajandar taron na kwana biyu.
Iran da Isra’ila sun fara yaƙi ne tsawon kwanaki takwas bayan da Isra’ila ta ce Iran na dab da mallakar makamin nukiliya, inda ta ƙaddamar da manyan hare-hare kan abokiyar gabarta, wanda kuma ya haifar da harin ramuwa daga gwamnatin Iran.
Tun da fari, Erdogan ya yi gargaɗin cewa yaƙin zai janyo ƙaruwar kwararar baƙi, yayin wata tattaunawar tarho da Wazirin Jamu Friedrich Merz.
Ya ce, "Tashintashinar da harin Isra’ila ya janyo zai cutar da yankin da kuma Turai ta ɓangaren baƙin haure da yiwuwar zubar sinadarin nukiliya, kuma ya yi gargaɗin cewa rikicin ya "ta’azzara barazanar rashin tsaro a yankin zuwa babban mataki".
Duk da ruwan bamabamai, wata majiyar ma’aikatar tsaron Turkiyya ta faɗa ranar Alhamis cewa “ba a samu ƙaruwar" masu haura iyakar ƙasar da Iran ba.
Yayin ziyararsa ranar Laraba, Ministan Tsaro Yasar Guler ya ce, "an inganta matakan tsaro a iyakokinmu".