A nasarar farko da ya samu a wasan da ya jagoranci Real Madrid, sabon koci Xabi Alonso ya yi waje da ƙungiyar Pachuca ta Mexico, a wasan kofin duniya na kulob-kulob da ke gudana a Amurka.
Jude Bellingham ɗan asalin Ingila da Arda Guler dan asalin Turkiyya sun ci ƙwallo guda-guda a farkon zangon wasan, bayan da aka kori ɗan wasan baya na Madrid, Raul Asencio tun a minti na 7 da fara wasa.
Sannan a minti na 70, Federico Valverde ya ciyo ƙwallo ta 3, sannan a minti na 80, ɗan wasan Pachuca, Elias Montiel ya rama ƙwallo guda. Madrid ta yi nasara da ci 3-1, ita kuma Pachuca ta faɗo daga gasar.
An buga wasan a yanayi na tsananin zafi a ranar Lahadi a birnin Charlotte da ke jihar North Carolina, wanda ya tilasta ba da hutun shan ruwa a duka zangon wasan biyu.
Wannan sakamakon ya bai wa Xabi Alonso nasararsa ta farko a matsayin kocin Madrid, bayan da a wasan farko na gasar suka yi canjaras da ci 1-1 da Al-Hilal ta Saudiyya ranar Laraba.
A yanzu Real Madrid na da maki 4 daga wasanni biyu a Rukunin H, wanda ke nufin za ta iya kaiwa matakin ‘yan-16, idan suka doke ko yi canjaras da RB Salzburg ranar Alhamis a jihar Philadelphia.
Baya da ƙura
Ɗan wasan gaba na Real Madrid, Jude Bellingham ya koka kan filayen wasannin da ake gudanar da gasar a Amurka, waɗanda ya ce ba gangariya ba ne.
Bellingham ya ce filayen ba su burge shi ba, kuma yana fatan ganin an inganta su gabanin babbar gasar kofin duniya da za a yi a Amurka. An buga wasan ne kan ciyawa ta roba a filin da gidan ƙungiyar Carolina Panthers ne.
Haka nan kuma, a bayaninsa na ƙarshen wasan, Alonso ya ce ɗan wasansu na baya, Antonio Rudiger ya yi ƙorafin cewa kyaftin ɗin Pachuca, Gustavo Cabral ya ci zarafin launin fatarsa a wasan.
Hakan ya faru ne a mintunan ƙarshe na wasan, inda Cabral ya zargi Rudiger da masa ƙeta, har ya kai ga zagin sa. Rudiger ya sanar da alƙalin wasa Ramon Abatti Abel game da batun.
Alƙalin ya nuna alamar cewa hukumar ƙwallo ta duniya, FIFA za ta binciki lamarin, duk da cewa shi Cabral ya musanta laifin, inda ya ce shi fa kawai ya zagi Rudiger ne da ce masa “matsoraci".