Uwargidan Shugaban Kasar Turkiyya, Emine Erdogan, ta yi kira ga Kiristocin duniya su dauki matsayi mai karfi don taimakawa wajen kawo karshen matsalar jinƙai a Gaza, tare da yin kira ga Vatican ta ba da goyon baya kan samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin mafita game da rikicin Isra'ila da Falasdinu.
"Na ji dadi sosai da samun damar ganawa da Fafaroma Leo XIV, Shugaban Addini na Darikar Katolika kuma Shugaban Kasar Vatican, yayin ziyarata zuwa Vatican don halartar wani taron tattalin arziki,' wanda Majalisar Kimiyyar Zamani ta Pontifical ta shirya," in ji Matar Erdogan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a kafafen sada zumunta bayan ganawar a ranar Laraba.
"Tattaunawarmu ta fi mayar da hankali kan matsalar jinƙai da ke ci gaba a Gaza," ta ce. "Mun yi musayar ra'ayoyi kan muhimmancin Kiristocin duniya su dauki matsayi mai karfi don cim ma tsagaita wuta mai dorewa da tabbatar da isar da taimakon jinƙai gaba daya."
Uwargidan Shugaban Kasar Turkiyya ta kara da cewa: "Na bayyana jin dadina game da goyon bayan Vatican kan samar da mafita ta kasashe biyu, wanda shi ne tushen zaman lafiya na adalci mai ɗorewa a Falasdinu."
Erdogan da Fafaroma Leo XIV sun kuma tattauna batutuwan muhalli yayin ganawarsu, musamman shirin "Zero Waste" na Turkiyya.
"Mun amince cewa matsalar yanayi wata damuwa ce ta bai daya ga dukkan bil'adama, ba tare da la'akari da addini ko yankin kasa ba," in ji ta.
"A cikin wannan yanayi, na jaddada babbar damar hadin-kai tsakanin Turkiyya da Vatican wajen yaƙi da sauyin yanayi. Mun yi nazari kan wuraren da za a iya yin aiki tare."
Ta kammala sanarwarta da godiya ga Fafaroma Leo XIV saboda "karimcin bakunci" da ya nuna, sannan ta kara da cewa: "Ina fatan nauyin tarihi da ya dauka zai kawo sakamako masu kyau ga duniya Katolika da dukkan bil'adama."