WASANNI
3 minti karatu
Najeriya, Senegal, Afirka ta Kudu sun yi kunne doki a wasannin share fagen shiga Gasar Kofin Duniya
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta buga wasa da Rasha a karon farko a gasar duniya, yayin da Zambia ta je baƙunci Ireland, ita kuma Afrika Kudu ta buga kunnen doki a gida.
Najeriya, Senegal, Afirka ta Kudu sun yi kunne doki a wasannin share fagen shiga Gasar Kofin Duniya
The match against Russia was the last of three warm-up matches for the Super Eagles. / Others
7 Yuni 2025

Manyan ƙasashen Afirka Najeriya da Senegal da Afirka ta Kudu sun tashi kunnen doki a wasannin sada zumunta da suka yi a ranar Juma'a, domin shirye-shiryen neman gurbin shiga gasar Cin Kofin Duniya ta 2026 da za a fara a watan Satumba.

Tolu Arokodare, wanda ya shiga wasan bayan hutun rabin lokaci, ya ci wa Nijeriya ƙwallonsa ta farko, inda aka tashi 1-1 da Rasha a birnin Moscow. Wannan shi ne karo na farko da ƙasashen biyu suka fafata a wasan ƙasa da ƙasa.

Ismaila Sarr, wanda ya lashe gasar FA Cup a Crystal Palace a watan da ya gabata, ya farke wa Senegal ƙwallo a wasan da suka tashi 1-1 da Jamhuriyar Ireland a birnin Dublin.

Afirka ta Kudu kuwa ba ta yi amfani da damar wasan gida ba, inda ta tashi babu ci da Tanzania a birnin Polokwane da ke arewacin ƙasar.

Najeriya da Afirka ta Kudu, waɗanda za su fafata a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a watan Satumba, sun kammala a matsayi na biyu da na uku a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2024, yayin da Senegal ta lashe gasar da ta gabata.

Super Eagles ta ci kanta

A birnin Moscow, ƙwallon da Semi Ajayi ya zura a ragarsu ta bai wa Rasha jagoranci a minti na 27, bayan ƙwallon da ya tura wa mai tsaron raga ta wuce shi ta shiga cikin zare.

Babu wata kwallo da aka kara har sai da mai tsaron ragar Rasha, Matvey Safonov, ya yi kuskure a minti na 71, inda Tolu Arokodare ya karɓi wata gajeriyar ƙwallo da Safonov ya yi niyyar bai wa abokin wasansa, sannan ya zura kwallo a ragar.

Wannan shi ne wasan sada zumunta na ƙarshe da Super Eagles ta yi, bayan ta lashe Unity Cup a birnin London makon da ya gabata, inda ta doke Ghana da ci 2-1 sannan suka doke Jamaica a bugun fanareti bayan sun tashi 2-2.

Rasha dai tana cikin takunkumin FIFA da UEFA tun shekarar 2022 sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine. Wannan shi ne karo na biyu da suka buga wasan sada zumunta da wata ƙasar Afirka a wannan shekara, bayan sun doke Zambiya da ci 5-0 a Moscow watanni uku da suka gabata.

Yunkurowar Senegal

A ɗaya bangaren, Senegal ta fara wasan ba tare da karsashi ba gabanin tafiya hutun rabin lokaci a birnin Dublin lokacin da Kasey McAteer ya zura kwallo a gara Senegal.

Senegal, wacce ta lashe gasar cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2022, ta farke kwallon a minti na 82 lokacin da Ismaila Sarr ya yi amfani da wata matsalar mai tsaron ragar Ireland, Caoimhin Kelleher, sannan ya zura kwallo a raga.

Senegal za ta ziyarci Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo a watan Satumba domin fafatawar da za ta tantance wacce ƙasa ce za ta samu gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya kai tsaye a Amurka, Kanada da Mexico.

A birnin Polokwane, Afirka ta Kudu ta fi riƙe ƙwallo, amma ba ta iya karya garkuwar tsaron Tanzania ba. Sun kusa zura kwallo a ƙarin lokacin da Relebohile Mofokeng ya yi ƙoƙarin jefa ƙwallo mai ban mamaki, amma ta sauka a saman ragar.

Zambiya ba ta samu damar buga wasan sada zumunta da Sudan a Maroko ba saboda yajin aikin 'yan wasan ƙasa kan rashin biyan alawus-alawus bayan wasan da suka yi da Rasha.

Sabon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, Keith Mweemba, ya shaida wa manema labarai cewa ya gaji wata hukuma da ke da bashin kwacha miliyan 100 ($4 miliyan).

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us