Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan ya ce ana tsammanin wani sabon zagaye na tattaunawar sulhu tsakanin Rasha da Yukrain yayin da ɓangarorin biyu suke ci gaba da yarda da buƙatar tattaunawa.
A wata tattaunawar da ya yi da TRT Haber ranar Talata, Fidan ya jaddada cewa yaƙin, wanda yake shiga shekararsa ta huɗu, ba kawai tsakanin ƙasashe biyu ba ne, amma ya rikiɗa ya zama yaƙi na duniya saboda sa hannun ƙasashen duniya.
Da yake sake jaddada adawar da Turkiyya ke yi da yaƙi, ya bayyana tarin asarar rayuka da tattalin arziƙi [da yaƙin ya jawo], inda aka kashe ko jikkata sama da mutum miliyan ɗaya tare da lalata muhimman birane.
Fidan ya bayyana jerin ƙoƙarin samar zaman lafiyar [da Turkiyya ke yi], ciki har da shirin jigilar hatsi na Bahar Aswad da tattaunawar Istanbul ta shekarar 2022 da kuma jerin yarjejeniyoyi na musayar fursunoni.
Ya bayyana cewa karɓuwar batun tsagaita ta yi ƙasa a lokacin gwamnatin Trump, kuma ya tuna ziyarar da shi kansa ya kai Moscow da Kiev.
Fidan ya ƙara da cewa ganarwa ta ranar 2 ga watan Yuni an yi ta ne cikin wani yanayi na fatan alheri, lamarin da ya samar da yarda da wani sabon shirin musayar fursunoni da ya ƙunshi mutane 1,000.
Ƙoƙarin Turkiyya na samar da zaman lafiya na din-din-din
Rasha da Yukrai ne suka gabatar da takardun da suka tsara yanayi na tsagaita wuta, kuma ɓangarorin sun yi musayar ra’ayi game yiwuwar ganawar shugabannin, in ji shi, yana mai cewa sun yarda da buƙatar da ke akwai na sake haɗuwa a zagaye na gaba na tattaunawar.
“Idan aka yi la’akari da yanayi na yanzu da kuma yanayi na ɗab’iu da yaƙin ya samar, wannan ita ce ganawa mafi inganci da za a iya samu. Muhimmin abu shi ne a bar teburin [sulhu] kuma ci gaba da ɗabbaka kiyaye tsagaita wuta da zaman lafiya.
Wannan ita ce shawararmu ga ɓangarorin.
Ko teburin na Turkiyya ne ko kuma wani wuri na daban ba shi ne muhimmin abu ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne waɗannan ɓangarorin sun ci gaba da haɗuwa suna tattaunawa,” in ji shi.
Fidan ya bayyana shiryawar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip na kasancewa mai masauƙin ganarwar shugabannin biyu, yana mai jaddada cewa Erdogan shi kaɗai ne shugaban da duk ɓangarorin uku suka yarda da shi.
“Za a iya samun wuri, amma a matsayinsa na shugaba na siyasa mai matsayi a duniya wanda ya shafe shekaru yana gwagwarmaya mai ƙarfi da aka sani da gaskiya da riƙon amana da kuma ƙwarrarun ma’aikatu, babu wani shugaba da ya cancanta,” in ji shi.
Fidan ya kuma ce ganawa kai tsaye tsakanin shugabannin Rasha da Yukrain zai zama dole idan aka samu ci-gaba a tattaunawa na gaba.
Ya ce tallafin Amurka ga Yukrain a ƙarƙashin Shugaba Joe Biden yana ci-gaba har yanzu, amma ana tsammanin zai zo ƙarshe cikin ‘yan watanni, inda bayan haka ne shawarwarin Shugaba Donald Trump za su iya sauya yadda yaƙin ke tafiya.
Yaƙar ta’addanci a Siria
Fidan ya kuma yi bayani game da sabon tsarin daƙile ƙungiyar ta’addanci Daesh, tsarin da ya ƙunshi Turkiyya da Siria da Iraƙi da Jordan da kuma Lebanon.
Ya ce a cikin ‘yan makonnin da suka wuce, an karɓi baƙuncin ministocin Jordan da Siria a Ankara, inda aka ɗauki wani mataki na kafa wani wuri na tattara bayanan sirri da aiki ta hanyar wakilan soji da jami’an tsaro na farin kaya.
“Tawagogi da suka ƙunshi jami’ai daga Jordan da Siria da kuma Turkiyya sun ƙaddamar da shirin na daƙile Daesh. Wannan wani babban mataki ne na samar da tsaro na yanki,” in ji shi.
Fidan ya ce ci-gaban da aka samu ƙalilan ne tun bayan yarjejeniyar haɗin kai da aka yi a ranar 10 ga watan Maris tsakanin gwamnatin Siria da ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG, wanda ke aiki da suna SDF a Siria, amma ya ce ana samun muhimmin ci-gaba a bayan fage.
Ya kuma ce sa hannun gwamnatin Amurka a Siria, da ababen da ke faruwa a ƙasa da kuma ƙoƙarin da Turkiyya ke yi suna ƙara haɗuwa.