WASANNI
1 minti karatu
Ivan Rakitic ya yi ritaya daga ƙwallo, zai fara aikin horarwa a tsohuwar ƙungiyarsa
Tsohon ɗan wasan Barcelona da Sevilla, Ivan Rakitic ya yi ritaya daga ƙwallon ƙafa, inda zai koma aikin ba da horo ga 'yan wasa.
Ivan Rakitic ya yi ritaya daga ƙwallo, zai fara aikin horarwa a tsohuwar ƙungiyarsa
Ivan Rakitic / TRT Afrika
2 Yuli 2025

Ivan Rakitic ya kawo ƙarshen rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, bayan ya kammala kakar bana a ƙungiyar Hajduk Split ta Croatia, inda zai fara aikin horarwa a kulob ɗin.

Tsohon ɗan wasan Barcelona da Sevilla ya yanke shawarar ci gaba da zama a Hajduk Split a matsayin mataimakin daraktan wasanni na ƙungiyar, Goran Vucevic.

Kocin Hajduk, Gonzalo Garcia ne ya sanar da ritayar ɗan wasan yayin da yake miƙa godiyarsa gare shi.

Rakitic ɗan asalin Croatia ne kuma ya bar buga ƙwallo ne yana da shekara 37. Ya fara wasa ne a ƙungiyar matasa ta Basel a Switzerland, kafin ya shiga babbar tawagar Basel.

Daga bisani, Rakitic ya koma Schalke ta Jamus, sannan ya tafi Sevilla ta Sifaniya, inda daga nan Barcelona ta ɗauke shi a 2014.

Shekara 6 bayan nan, ya koma Sevilla, sannan ya buga wa ƙungiyar Al-Shabab ta Saudiyya. Daga nan ne ya sake komawa gida ƙungiyarsa ta farko, wato Hajduk Split.

A kakarsa ta ƙarshe, Rakitic ya ci ƙwallaye biyu, da tallafin ƙwallaye biyar cikin wasanni 39 a duka gasanni.

A yanzu ana sa ran Ivan Rakitic zai taimaka wa ƙungiyar Hajduk Split wajen ba da shawarwari kan ɗaukar ‘yan wasa da sauran harkokin wasanni.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us