Wani gungun 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 40 daga cikin kungiyoyin ‘yan banga na ƙauyuka a wani kwanton ɓauna da kuma hare-hare da suka faru a karshen mako a jihar Filato ta tsakiyar Nijeriya, in ji Hukumar Agajin Gaggawa ta Red Cross da mazauna yankin ranar Talata.
Wani mazaunin yankin ya bayyana hare-haren a matsayin wani nau'in "ramuwar gayya" kan kungiyoyin tsaron kai na yankin da aka kafa don kare al'umma daga hare-haren 'yan bindiga.
Shekaru da dama, wadannan 'yan bindiga sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a yankunan karkara na arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya inda babu isasshen tsaro daga gwamnati, suna kashe dubban mutane da kuma yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Sakataren Red Cross na jihar Filato, Nuruddeen Hussain Magaji, ya ce "daruruwan 'yan banga sun fada tarkon kwanton ɓaunar" a ranar Lahadi, inda aka kashe mutum 30 a ƙauyen Kukawa.
Wannan harin ya faru ne bayan da 'yan bangan suka sake taruwa bayan wata arangama da ta faru a safiyar ranar a ƙauyen Bunyun Nyalum, inda aka kashe 'yan banga 10, kamar yadda wani mazaunin yankin, Musa Ibrahim, ya bayyana.
Usman Nyalum, wani mazaunin yankin, ya ce harin da aka kai Bunyun Nyalum ya biyo bayan wani sabon yunƙuri na 'yan banga a yankin wanda ya yi sanadin kashe 'yan bindiga da dama.
"Tun bayan kashe 'yan bindiga da 'yan banga suka yi, sauran 'yan bindiga suna ci gaba da kokarin ɗaukar fansa," in ji shi.
Magaji, jami'in ƙungiyar Red Cross, ya gargadi cewa adadin wadanda suka mutu na iya ƙaruwa saboda "za a ci gaba da gano gawarwakin 'yan bangan a cikin daji."
Jami'ai da mazauna yankin sun tabbatar da hare-haren da suka faru a daren, duk da cewa ba a samu cikakken adadin wadanda suka mutu ba.
Rashin isasshen tsaro
Jihar Filato da ke fama da rikice-rikice a Nijeriya tana yawan fuskantar rikice-rikicen kisan kai tsakanin makiyaya da manoma kan filaye da albarkatun kasa.
Yawancin tashin hankali a Filato yana faruwa ne a wuraren da babu isasshen tsaro daga gwamnati, wanda ke bai wa masu aikata laifi damar aikata ayyukansu ba tare da tsoro ba, in ji masu sharhi.
Kafa kungiyoyin tsaro na gwamnati da kuma 'yan banga na tsaron kai ya fadada tsarin tsaron Nijeriya ta hanyoyi daban-daban, amma sakamakon ya kasance wanda kowanne angare ke ji a jikinsa.
A watan Yuni, 'yan banga da gwamnati ke goyon baya sun kashe fiye da 'yan bindiga 100 a wani artabu a jihar Zamfara da ke arewa maso yamma.
Tare da goyon bayan gwamnati, sun kai hari maboyar Bello Turji, wani sanannen shugaban 'yan bindiga, duk da cewa ya tsere.
Duk da kokarin sojoji, 'yan sanda da kungiyoyin tsaron kai, ana ci gaba da samun tashin hankali a fadin yankunan karkara na Nijeriya, daga 'yan bindiga har ma da 'yan ta'adda, wadanda sansaninsu yake a arewa maso gabas.
Kungiyoyin ‘yan sa-kai na cikin gida sau da yawa suna fuskantar matsin lamba ko kuma ramuwar gayya mai tsanani daga 'yan bindiga saboda kokarin da suke yi na kare kansu.
Ko da yake 'yan bindiga ba su da wata manufa ta aƙida kuma suna yin ayyukansu ne don samun kudi, hadin kansu da 'yan ta'adda da ke ƙara ƙarfi na zama abin damuwa ga hukumomi da masu nazarin tsaro.