Ɗan wasan gaba na AS Roma ta Italiya, Tammy Abraham ya isa birnin Istanbul domin kammala shirin komawa ƙungiyar Besiktas ta Turkiyya.
Abraham mai shekaru 27, wanda ke da kwantiragi da Roma ya samu kyakkyawar tarba daga mataimakin shugaban Besiktas, Murat Kılıç, da magoya bayan ƙungiyar a filin jirgin sama na Istanbul a daren Talata.
Ɗan wasan ɗan asalin Ingila ne mai tsatso a Nijeriya zai yi gwajin lafiya a wani ɓangare na shirin.
Besiktas ta tabbatar a hukumance a ranar Talata cewa an fara tattaunawa da Abraham da AS Roma kan batun sauyin sheƙarsa.
Rahotanni daga Italiya na nuna cewa tattaunawar ta shafi yarjejeniyar aro ga ɗan wasan, wanda yake da shekara guda a kwantiraginsa a Roma.
Ƙwarin gwiwar Abraham
Da isowarsa Istanbul, Tammy Abraham ya bayyana farin cikinsa ga Besiktas TV, inda ya nuna sha'awarsa ga sabon babin rayuwarsa ta wasa.
"Na yi tafiya mai tsawo a rayuwata ta wasa. Ina matuƙar farin ciki," in ji Abraham. Na taɓa zuwa Turkiyya a baya, amma ban taɓa zuwa Istanbul ba. Babban abu ne kasancewa a Istanbul. Turkiyya ƙasa ce mai ban mamaki. Ina farin ciki sosai yanzu."
Sanye da rigar Besiktas mai launin baƙi da fari, Abraham ya ƙara da cewa, "Ina ganin wannan riga a talabijin koyaushe. Yanzu lokaci ya yi da zan sanya ta. Ina matuƙar farin ciki da jin daɗi."
Ya jaddada burinsa na nasara da kuma sha'awarsa ga tarihin ƙungiyar da magoya bayanta.
Cikakken sunan Abraham, Kevin Oghenetega Tamaraebi Bakumo-Abraham, kuma an haife shi a Camberwell, gundumar Greater London. Amma iyayensa 'yan Nijeriya ne.
Abraham ya koma AS Roma a watan Agustan 2021 daga Chelsea kan kuɗi na euro miliyan 41.
Ya taka muhimmiyar rawa a nasarar Roma a gasar Europa Conference League a shekarar 2022. Ya je aro AC Milan a kakar 2024-25, inda ya zura ƙwallaye 10 a duka gasanni.