Yayin da gwamnatin Netanyahu ta so kawo sauyin gwamnati a Tehran, hare-haren Isra'ila ya zuwa yanzu sun haifar da gagarumin tasiri a duk faɗin Iran. Kuma ɓangarorin biyu na ci gaba da auna zaɓin abin da za su yi a nan gaba a ƙarƙashin gwamnatin Trump da ba ta da tabbas.
Ko shakka babu Iran, ƙasar da ta daɗe tana daƙile barazanar Isra'ila ta hanyar ƙawayenta irin su Hizbullah da tsohuwar gwamnatin Assad na Syria, ta sha wahalar kan yadda maƙiyanta ke kai mata hari da hantarar ta tare da goyon bayan Amurka. Dole ne Iran ta saka ido, yayin da ta yi asarar manyan kwamandoji da masana kimiyyar nukiliya.
Amma gwamnatin Netanyahu mai tsattsauran ra'ayi ita ma ba za ta iya yin iƙirarin samun cikakkiyar nasara kan Iran ba, duk da yadda ya saba nunawa duniya. Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ali Khamenei bai nuna ja da baya ba daga ainihin matsayinsa, duk da cewa an tilasta masa zama a ƙasan wani tsauni.
Babu yiwuwar samun sauyin shugabanci a Iran," in ji Charles Parton, wani tsohon babban jami'in diflomasiyyar Birtaniya kuma mamba a Majalisar Harkokin Ƙasa da kuma Cibiyar Ayyukan Soji ta Royal United Services Institute (RUSI), manyan cibiyoyin bincike da siyasa na Birtaniyya.
Hare-haren Isra'ila, waɗanda da farko gwamnatin Trump ke marawa baya, ko da yake daga baya ta matsa wa Isra'ila lamba ta amince da tsagaita wuta, ba za su haifar da wani tsari na siyasa a Tehran ba wanda zai janyo gwamnati ta rushe ta faɗa hannun Yammacin duniya,," Parton ya shaida wa TRT World, yana mai nuni da burin Yahudawa masu tsananin kishin ƙasar Isra’ila da na Yammacin Turai na maye gurbin gwamnatin da ke ci yanzu a Iran.
Wannan kuma ya nuna wani yanayi marar daɗi ga gwamnatin Netanyahu, wanda tsawon shekaru da dama da ke yakin neman zaɓe da alƙawarin za ta kifar da gwamnatin da aka kafa bayan juyin juya halin 1979 a Tehran, amma bai yi nasara ba duk da hare-haren kai-tsaye da Isra'ila da Amurka suka kai kan Iraniyawa da suka haɗa da cibiyoyin nukiliyar ƙasar.
Ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna a yanzu suna ta fama da tasirin bayan yaƙin da suka gwabza a baya-bayan nan. A cikin gajeren lokaci, kakkausan martani daga Trump game da karya yarjejeniyar tsagaita wuta na iya zama matakin da ya dakatar da rikicin baya bayan nan tsakanin abokan hamayyar a yankin. Amma a tsawon lokaci, makomar Tehran da Tel Aviv ta ta'allaƙa ne kan yadda dukkan ɓangarorin ke kallon zaman lafiyar da ake da shi mai rauni.
Yayin da tunkaar juna tsakanin Isra'ila da Iran ta zama matsala ta tsawon lokaci, gazawar Isra'ila na kawo sauyin gwamnati a Tehran ya nuna irin kalubalen da gwamnatin Netanyahu ke fuskanta, tun daga yaƙin da take yi a Gaza zuwa manufofin mamaya a Gabar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, a ƙarshe kuma da dabarun yaƙar Iran da ba sa tasiri da take da su.
To waye ya yi nasarar yakin na kwanaki 12?
Yayin da bangarorin biyu sun fuskanaci asara mai yawa tare da 'yan nasarori, yakin na kwanaki 12 bai samar da wata nasara bayyananniya ga kowane ɗaya daga cikin su ba.
A maimakon haka, ya zama wuri na shirya “gwagwarmaya ta dogon lokaci” tsakanin ƙasashe biyu masu aƙidu da ra’ayoyin siyasa daban-daban, a cewar Andreas Krieg, mataimakin farfesa a King’s College London kuma daraktan MENA Analytica.
“Nasarar ayyukan soja tana ga Isra’ila. Amma juriya mai ɗorewa da kuma gawurtacciyar turjiya, sun karkata ga Iran. Babu ɓangaren da ya cim ma matsaya mai ma'ana ko cikakkiyar nasara, abin da ya bar yankin cikin yanayi na rashin tabbas da ba a warware ba. Dukansu suna da'awar ‘nasara,’ amma a gaskiya, sun kasance cikin wata babbar gasa inda har yanzu babu wanda ya zarce ɗayan ta fuskar ƙarfi,” in ji Krieg ga TRT World.
Yayin da hare-haren da Isra'ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran suka yi kamar sun jinkirta shirin sarrafa uranium na Iran, ba su cim ma "manyan burinka da ba kamar kawo cikas ga gwamnati," kamar yadda Jamil ya shaida wa TRT World. A gefe guda kuma, Iran ta samu damar kiyaye "jagorancinta na asali," duk da asara a tattalin arziki da ta soja, kamar yadda ta bayyana.
Duk da cewa dukkan ɓangarorin biyu sun yi babbar asara ba tare da wasu nasarori ba, yakin kwanaki 12 bai bayar da wata nasara ga kowannen su ba.
Maimakon haka, yakin ya zama filin dagar gwada ƙwanjin gwagwarmayar da aka daɗe ana yi tsakanin ƙasashe biyu da ke da mabanbantan aƙida da siyasa, a cewar Andreas Krieg, wani farfesa a Kwalejin King London kuma daraktan MENA Analytica.
"Nasarar kai hare-hare na ga Isra'ila. Amma juriya cikin dabaru da da nuna tirjiya na koma wa ga bangaren Iran. Babu wani bangare da ya cim-ma nasara baki daya, wanda ya bar yankin a cikin hali mai rauni da rashin tabbas. Kowanne bangare na ikirarin samun nasara, amma magana ta gaskiya, suna cikin yanayin da ba za a ce wani ya shammaci ɗayan tare da yin nasara a kan sa ba.
Aimen Jamil, ƙwararriya kan al'amuran Iran da ke Islamabad, ta yi irin wannan tsokaci, tana mai cewa "rikicin bai haifar da nasara ba a fili."
Yayin da Isra'ila da Amurka ke kai hare-hare kan cibiyoyin Nukiliya na Iran don kawo cikas ga sarrafa Uranium da Iran ke yi, ba su cim ma manyan buri irin na taɓarɓarawa da hargitsa gwamnati ba," kamar yadda Jamil ta shai da wa TRT World. Ta ƙara da cewa, a ɗaya ɓangaren, Iran ta iya kare shugabancinta amma fa ta tafka asarar tattalin arziki da soji.
A yayin yakin na kwanaki 12, Isra'ila ta nuna karfinta na kai hare-hare kan Iran, kamar dai yadda ta yi kan sauran abokan hamayyarta a yankin, tun daga Hezbollah zuwa Houthi, waɗanda su ma gwamnatin Netanyahu ta afka wa yankunansu.
Waɗannan hare-haren da aka kai sun bai wa Isra'ila damarmakin soji, yayin da ta asarar da ta yi ba ta da yawa.
Duk da haka, ga gaskiyar lamarin abin ke faruwa ta ƙara fitowa fili: Ƙarfin sojin Isra’ila bai warware matsalar siyasa da tsaron ƙasa daga Iran ba, abin da ke nufin har yanzu ba a warware rikicin ba kenan.
Duba nasarar ta mahanga uku
Cikakken nazari da duba kan yakin na kwanaki 12 "ya dogara ne akan yadda mutum ya kalli rikice-rikicen ta mahanga uku na nasara: Amfana, Ƙarfin yanke hukunci, da Nasara," in ji Krieg, kuma manazarci kan al’amuran da suka shafi tsaro.
Dangane da amfana, za a iya cewa Isra'ila ce a kan gaba saboda kawar da wasu manyan janar-janar na Iran, da lalata kayayyakin makamashin nukiliya na Tehran, da suka haɗa da cibiyar Fordow mai girma da ke ƙarƙashin ƙasa, da kuma katse hanyoyin tabbatar da jagoranci, in ji Krieg.
"A dabarance, wannan 'nasara' ce ga Isra'ila, duk da cewa ta yi asarar kuɗi sosai da kuma fuskantar matsala a cikin gida.” in ji shi.
Amma idan aka kalli batun ta mahangar manyan dabaru, za a cewa yanayin bai fito sosai ba, in ji shi. "Ma'aunin ya karkata ga juriyar da Iran ta nuna, idan ba a ce nasararta ba. Duk da gwamnatin Iran ta jure hare-hare daga Amurka da isra’ila, ta nuna ikon jure bala’o’i, da magance rikicin cikin gida, da ci gaba da samun karfin fada a ji a yankin ta hanyar wakilanta da take ɗaukan nauyinsu.”
Har ila yau Krieg ya bayar da haske game da halin "jure-hatsari" da gwamnatin Iran ke nuna wa, wanda ya sanya ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar. Iran ta ce ba ta tsoro ko shakkar ɗaukar matakan ba sani ba sabo ko ma me za su janyo, inda ta yi nuni ga mayaƙanta na Juyin Juya Hali.
Yayin da zazzafan rikici tsakanin Iran da Isra'ila ke ci gaba da ƙaruwa, masana a fannin, ciki har da Krieg, sun yi gargaɗi game da matasa masu tsattsauran ra'ayi na IRGC, masu zuciyar tarar aradu da ka.
A kan ma'aunai masu mahimmanci, Iran ta nuna iyawarta ta "tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro" da nuna "juriya," tana mayar da kanta "ba kawai a matsayin wadda za a kai wa hari ba, a’a mai mayar da martani da tunkarar kasada,,” a ra’ayin Krieg.
Yayin da damarmakin kai farmakan Isra'ila suka "disashe" ƙoƙarin mamaya da Iran ke son yi, wannan nasara ce da gwamnatin Netanyahu za ta iya cewar ta samu, amma ba ta cika burinta ba, ta yi wa Iran illa, amma ba ta kawar da matsayin Iran a yankin ko hana ta burin mallakar Nukiliya ba.
A kan ma'aunin yanke hukunci, binciken Krieg ya nuna cewa yaƙin na kwanaki 12 zai iya bayar da sakon "rashin kwanciyar hankali" a cikin siyasar yankin, kuma ba tare da samun wata takamaimiyar hanya ta wareware rikicin ba.
Idan Iran za ta iya sake gina tushen karfinta, da na wakilanta a duk faɗin yankin, wannan na iya haifar da "taɓarɓarewar yanayin da ake ciki."
"Tsagaita wuta ta wucin gadi da aka ƙulla ta ƙasashen Yankin Tekun Fasha na da rauni, don haka yiwuwar ɗaukar mataki ya ragu a dukkan ɓangarorin biyu," in ji shi.
A ƙarshe, dangane da nasara, rikicin na baya-bayan nan na nuni da cewa "an yi kunnen doki, inda Isra'ila ta zira ƙwallaye mafi yawa a ɓangaren dabarar yaƙi, ita kuma Iran ta riƙe matsayinta yankinta a dabarance," a cewar Krieg.
"Isra'ila ba ta yi asara ba amma kuma ba a yi nasara a kanta ba, Iran ta kauce wa shan kaye, ta kuma kiyaye zaɓin abin yi da ya dace, don haka za ta iya da'awar cewa ‘babu asara' daga ɓangarenta."