NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 30 sakamakon hare-haren 'yan bindiga
'Yan bindigar sun kashe mutum 16 a Tadurga sai kuma 14 sun rasu a Kyebu da ‘Yar-Kuka dukansu da ke yankin Masarautar Zuru a Jihar Kebbi.
Gwamnatin Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 30 sakamakon hare-haren 'yan bindiga
Maharan sun tsere da dabbobi da sauran muhimman abubuwa. / REUTERS
21 Yuni 2025

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutum 30 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a kan al’ummomin Zuru.

Shugabannin Ƙananan Hukumomin Zuru da Danko Wasagu ne suka tabbatar da hakan a wata ziyarar da Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida ya kai Tadurga da Gajere da Bena a ranar Juma’a.

Muhammad Gajere da Hussaini Bena sun bayyana cewa an kashe mutum 16 a Tadurga sai kuma 14 sun rasu a Kyebu da ‘Yar-Kuka da ke gundumar Waje, kamar yadda gidan talabijin na Channels a Nijeriya ya ruwaito.

Sun kuma bayyana cewa maharan sun tsere da dabbobi da sauran muhimman abubuwa.

Sanata Tafida ya jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa waɗanda duka ke ƙarƙashin masarautar Zuru dangane da iftila’in da ya afka musu

Haka kuma mataimakin gwamnan ya bai wa al’ummomin Tadurga da Kyebu naira miliyan 25 kowanensu domin taimaka wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan lokaci.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fama da matsalar tsaro a Nijeriya musamman matsalar ‘yan fashin daji da kuma mayaƙan Boko Haram.

Duk da cewa jami’an tsaron Nijeriya na iƙirarin samun nasara a kan ‘yan bindigar, amma har yanzu suna ci gaba da cin karensu ba babbaka a wasu sassan ƙasar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us