NIJERIYA
2 minti karatu
Me Shugaba Tinubu na Nijeriya ya je yi taron BRICS a ƙasar Brazil?
Fadar Shugaban Nijeriya ta ce Shugaba Tinubu zai yi jawabi kan irin gyare-gyaren da yake yi a Nijeriya domin ɗora ƙasar bisa saiti, da kuma jawo masu zuba jari na ƙasashen duniya su zuba jari a Nijeriya ta ɓangaren noma da kiwon lafiya da makamashi.
Me Shugaba Tinubu na Nijeriya ya je yi taron BRICS a ƙasar Brazil?
Shugaban zai halarci wata ganawa da Lula zai jagoranta, kafin babban taron da za a fara daga ranar 6 zuwa 7 ga Yuli. / Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya
5 Yuli 2025

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya isa birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil, domin halartar taron shugabannin ƙasashe da gwamnatoci karo na 17 na ƙasashen BRICS waɗanda suka haɗa da Brazil, Rasha, India, China, da Afirka ta Kudu.

Jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin saman soji na Galeao da misalin ƙarfe 8:45 na dare a ranar Juma’a, inda Kwamandan filin jirgin sojin ya jagoranci gaisuwar ban girma ta soji, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan watsa labarai Bayo Onanuga ta tabbatar.

Mataimakin Ministan Brazil mai kula da harkokin Afirka da Gabas ta Tsakiya Ambasada Carlos Sergio Sobral Duarte, da kuma Mataimakin Ministan Brazil kan Harkokin Tattalin Arziki, Kimiyya, Fasaha, Kirkire-kirkire da Al'adu, sun tarbi Shugaba Tinubu a wajen saukar jirgin.

Shugaba Tinubu yana Brazil ne bisa gayyatar Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula Da Silva. Shugaban zai halarci wata ganawa da Lula zai jagoranta, kafin babban taron da za a fara daga ranar 6 zuwa 7 ga Yuli.

A yayin taron BRICS, Shugaba Tinubu zai halarci zaman taron koli kuma zai gabatar da jawabi kan gyare-gyaren da yake yi a Nijeriya domin mayar da tattalin arziƙin ƙasar bisa saiti, kamar yadda sanarwar Bayo Onanuga ta bayyana.

Haka kuma, ana sa ran shugaban zai buƙaci masu zuba jari na ƙasashen duniya su yi amfani da damar da ake da ita a Nijeriya a fannoni kamar noma, ma’adanai, lafiya da makamashi domin su zuba jari.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us