Rahotanni daga Real Madrid na bayyana cewa ƙungiyar ta yanke hukuncin bayar da aron matashin ɗan wasanta, Endrick a kakar wasan da za a shiga nan da makonni.
Tuni alamu suka nuna cewa sabon kocin Madrid, Xabi Alonso ba shi da niyyar amfani da Endrick a tawagarsa. Don haka zai fi kyau ga ɗan wasan ya nemi mafita a waje.
Duk da cewa ɗan wasan ɗan asalin Brazil yana da burin ci gaba da kasancewa a Madrid, bayanai sun ce ba zai buga kakar 2025-2026 a can ba.
Endrick zai cika shekara 19 a wannan watan, kuma ya nuna hazaƙa a lokutan da ya samu damar buga wasa ƙarƙashin tsohon Koci Carlo Ancelotti, duk da ya yi ta ɗumama benci.
Sai dai ƙarƙashin Alonso, Madrid na ganin Endrick zai ci gaba da kasancewa a benci, ganin bai samu buga wasa a makonnin farko na Gasar Kofin Duniya na kulob-kulob ba.
Amma duk da cewa jinya ce ta hana Endrick buga wasa a gasar da ke gudana a Amurka, a madadinsa Gonzalo Garcia ya buga duka wasannin da Real Madrid ta buga zuwa yanzu.
Hasali ma Garcia ne ke kan gaba a jadawalin cin ƙwallaye a gasar, inda ya ci ƙwallaye huɗu da tallafin ƙwallo ɗaya a wasanni biyar.
Rashin gurbi
Tawagar Real Madrid ta cika inda a gaba ake da Gonzalo Garcia, Kylian Mbappe, Vinicius Junior, Jude Bellingham, da Arda Guler, wanda ke nufin Endrick zai yi ta jiran tsammani ne a kaka mai zuwa.
Ko a ‘yan lokutan da Alonso ya yi atisaye da Endrick, kocin ya yi yunƙurin sauya masa gurbi, inda yake gwada shi a matsayin ɗan wasan gefen dama.
A yanzu rahotanni na cewa ƙungiyoyi a Jamus da Faransa waɗanda a baya suka nuna sha’awar ɗauko Endrick a matsayin aro suna fara shirin sake miƙa buƙatarsu.
Sakamakon haka, Endrick ya zanta da wani babban jami’in Real Madrid, Jose Angel a Amurka don nema masa makoma.
Amma sai a makonni masu zuwa ne za a samu sanarwa a hukumance kan abin da Real Madrid ta yanke a ƙarshe.