GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Ƙasashe sun 'shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya' in ji Rasha
Wani babban jami’in Rasha Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan Amurka ta kai hare-haren bama-bamai kan tashoshin nukiliyar Iran.
Ƙasashe sun 'shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya' in ji Rasha
Wani babban jami’in a gwamnatin Rasha, ya ce wasu ƙasashe sun shirya domin goyon bayan Iran a yaƙinta da Isra’ila / Reuters
23 Yuni 2025

A ranar Lahadi wani babban jami’in Rasha Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyar Iran.

“Wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliyarsu kai-tsaye,” kamar yadda Medvedev, Mataimakin Majalisar Tsaron Rasha, ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a Telegram.

Kalaman nasa na zuwa ne sa’o’i bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi shelar cewa dakarun Amurka sun kai hare-haren bama-bamai kan tashoshin nukiliya a Fordow da  Natanz da kuma Isfahan. Hare-haren sun nuna yadda rikicin Iran da Isra’ila ke kara taɓarɓarewa.

Medvedev ya ce da alama wuraren da aka kai wa hare-haren ba su ba lalalce sosai, yana mai ƙarawa da cewa inganta yuraniyum da kuma samar da makaman nukiliya ka iya ci gaba.

Rasha ta ce 'yawancin ƙasash' suna adawa da matakan Amurka da Isra’ila a kan Iran

Ya yi gargaɗin cewa Amurka ta sake “shiga” wani babban rikici, a wannan karon “da alamar [za ta yi] wani aiki [hari] na ƙasa,” kuma ya ce shugabannin Iran sun ƙara ƙarfi sakamakon hare-haren.

“Mutane suna mara wa shugabancin addinin baya, har ma da waɗanda ba sa sonta [a da],” in ji shi.

Ya soki Trump kan sake ƙaddamar da wani yaƙi duk da cewa ya yi yaƙin neman zaɓe ne a matsayin mai “samar da zaman lafiya,” inda ya yi watsi da yiwuwar shugabn na Amurka ya samu lambar yabon Nobel ta zaman lafiya.

Medvedev ya kuma yi iƙirarin cewa “yawancin ƙasashe” suna adawa da matakan Amurka da Isra’ila.

An kashe ɗaruruwa a Iran, gommai a Isra’ila

Hare-haren Amurka sun biyo bayan zafafan hare-haren Isra’ila kan Iran wanda ta fara ranar 13 ga watan Yuni. Tehran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami kan biranen Isra’ila da sansanonin soji.

Ma’aikatar lafiyar Iran ta ce an kashe aƙalla mutum 430 kuma aka jikkata mutum 3,500 a hare-haren Isra’ila. Hukumomin Isra’ila sun ba da rahoton cewa mutum 25 sun mutu inda ɗaruruwa suka ji rauni sakamakon hare-haren ramuwar gayyar Iran.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us