AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin Sudan sun ƙara ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum
Sojojin Sudan sun ce sun halaka abokan gabarsu tare da ƙwace ɗumbin kayayyakinsu da makamansu
Sojojin Sudan sun ƙara ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum
RSF ta ƙwace iko da fadar shugaban Sudan a ranar 1 ga Mayun 2023 / AFP
21 Maris 2025

Rundunar Sojin Sudan ta bayyana cewa ta sake ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar da ke Khartoum a ranar Juma’a bayan gwabza yaƙi da rundunar RSF.

“Dakarunmu sun halaka abokan gabarmu da kayayyakinsu, da ƙwace ɗumbin kayayyakinsu da makamai,” kamar yadda mai magana da yawun soji Nabil Abdallah ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar ta talabijin ɗin ƙasar.

Abdallah ya sha alwashin cew sojojin za su “ci gaba da samun ci gaba a duka fagagen daga har sai sun samu nasara baki ɗaya da kuma tabbatar da cewa an kawar da duk wasu mayaƙa da magoya bayansu daga ƙasarmu”.

A shafukan sada zumunta, sojoji sun yi ta yaɗa bidiyo da ke nuna cewa suna cikin fadar shugaban kasa, inda suke taya juna murna.

 Ƙungiyar RSF ta ƙwace iko da fadar shugaban ƙasar a Afrilun 2023, bayan yaƙi ya ɓarke tsakaninsu da sojoji.

A lokacin, sai dakarun RSF suka yi saurin ƙwace iko da titunan Khartoum, inda sojojin ƙasar suka tsere zuwa Port Sudan da ke gaɓar Bahar Maliya.

Tsakiyar birnin Khartoum, wanda a nan ne fadar shugaban ƙasa tare da sauran ma’aikatu suke da manyan ma’aikatu, ya kasance fagen daga tsakanin sojojin da dakarun RSF.

A cikin kusan shekara biyu da aka shafe ana rikici tsakanin ɓangarorin biyu, ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da raba fiye da mutum miliyan 12 da muhallansu.

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us