‘Yan tawayen M23 da suka ƙaddamar da hare-hare a gabashin Kongo sun yi garkuwa da mara lafiya aƙalla 130 daga asibitoci biyu a birnin Goma, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ranar Litinin.
Mayaƙan M23 sun kai farmaƙi asibitocin CBCA Ndosho da Heal Africa ranar 28 ga watan Fabrairu da daddare, inda suka kama mutum 116 a asibiti na farko kuma suka kama mutum 15 asibiti na biyu, in ji mai magana da yawun ofishin kare hakkin ɗan’adam na MƊD Ravina Shamdasani a wata sanarwa.
An yi tunanin cewa mutanen da aka sace ɗin sojojin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ne ko kuma mayaƙan sa-kai da ke goyon bayan gwamnati da ake kira Wazalendo.
"Abu ne mai taƙaici matuƙa cewa M23 tana kama mara lafiya daga gadajen asibiti kuma tana garkuwa da su a wuraren da ba a bayyana ba," in ji Shamdasani, yana mai kira da a sake su nan-take.
Ma’adinai masu daraja
Masu magana da yawun M23 Willy Ngoma da Lawrence Kanyuka Kingston ba su ba da amsa nan-take ba a lokacin da aka nemi su yi tsokaci kan batun.
‘Yan tawayen sun shiga cikin birnin Goma ne bayan watan Janairu kuma sun yi irin kutsawar da ba su taɓa yi a gabashin Kongo ba, inda suka ƙwace iko da wani ɓangare kuma suka samu hanyar samun ma’adinai masu daraja.
Kutsawar da suke yi, wadda suka fara a ƙarshen watan Disamba, ita ce mafi muni a rikicin da ya samo asali daga kisan kiyashin Rwanda na shekarar 1994 da ya fantsama cikin Kongo tare da ƙoƙarin iko da ɗimbin ma’adinan Kongo.
Gazawar ƙoƙarin zaman lafiya
Gwamnatin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da masanan MƊD da kuma ƙasashen Yammacin Duniya na zargin Rwanda da tallafa wa wannan ƙungiyar.
Rwanda ta musanta zargin kuma ta ce tana kare kanta ne daga mayaƙan Hutu da ke da burin kashe ‘yan ƙabilar Tutsi a Kongo tare da yin barazana ga Rwanda.
Fiye da mutum 8,500 aka kashe a gabashin Kongo tun watan Janairu kuma kusan mutum rabin miliyan aka raba da muhallansu bayan an lalata sansanin ‘yan gudun hijira 90 a yaƙin, in ji gwamnati.
Takunkumin ƙasa-ƙasa da binciken da kotun hukunta manyan laifuka ta sabunta da kuma yarjejeniyar zaman lafiyar da Afirka ke jagoranta sun gaza tsayar da kutsawar ‘yan tawayen, waɗanda suka kama manyan biranen gabashin Kongo guda biyu, Goma and Bukavu.