Tun daga shekarar 1967, Tel Aviv ta kama kuma ta tsare kimanin Falasdinawa miliyan ɗaya — a ƙiyasi ana kama mutane 47 a kowace rana — yayin da tsarin gidajen yarin Isra'ila ke ci gaba da zama "ginshikin mamayarta" a Falasɗinu, kamar yadda wani sabon rahoto daga ƙungiyar American Muslims for Palestine ya bayyana.
A cewar rahoton, "A tarihi, mutanen da Isra’ila ke tsarewa a gidajen yarinta ba sa yin ƙasa da 6,000 a lokacin guda, wanda ke sauyawa yayin da ake samun rikice-rikice, amma yana komawa matsakaici cikin sauri.
Adadin ya karu sau bakwai bayan Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙin kisan ƙare dangi kan Gaza a watan Oktoba 2023, inda adadin sabbin wadanda aka tsare — waɗanda yanzu suka kai kusan kashi ɗaya bisa uku na duk Falasdinawan da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila — ya ƙaru daga 350 zuwa 2,373 a kowace wata.
Rahoton ya kuma jaddada yadda Tel Aviv ke aiwatar da tsarin tsare mutane ta hanyar taƙaita zurga-zurga da kuma dokoki masu tsauri, a matsayin wani bangare na tsarin da ke samun goyon baya daga kudade, da makamai, da kuma kariyar diflomasiyya daga Amurka.