Shugaban Rwanda ya bayyana cewa ƙasarsa za ta cika alkawuran da aka cim ma a yarjejeniyar zaman lafiya da aka ƙulla tsakanin ƙasarsa da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC), wanda Amurka ta shiga tsakani wajen tsara ta.
Wannan shi ne karo na farko da Paul Kagame ya yi magana a bainar jama'a tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar a Washington, wacce mutane da dama ke fatan za ta kawo ƙarshen rikicin da ke addabar gabashin DRC.
A yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Kigali ranar Juma’a, Kagame ya gode wa gwamnatin Amurka bisa shiga tsakani wajen tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiyan. Ya ce gwamnatin Trump ta yi duba kan abubuwa uku masu muhimmanci da suka haɗa da siyasa, da tsaro, da tattalin arziki.
Yarjejeniyar da aka cim ma ranar 27 ga watan Yuni ta tanadi dakatar da rikici tsakanin sojojin ƙasashen biyu da ke maƙwabtaka.
Ya kuma mayar da hankali kan manyan damuwar DRC, ciki har da mutunta cikakken yancin ƙasar, da kwance damarar ƙungiyoyin 'yan bindiga, da kuma aiwatar da matakan da za su dawo da dawwamammen zaman lafiya a yankin.
Kagame ya ce: "Mun amince da yin wasu abubuwa tare da wasu, kuma za mu yi hakan. Ba za ku taɓa samun Rwanda tana karya alƙawarin da muka yi ba, ba za ku taɓa samu ba. Amma idan ɗaya ɓangaren wasa suke yi da yaudara kuma suka dawo da matsalar, to za mu fuskanci matsala kamar wacce muke fama da ita yanzu haka."
Ya kuma jaddada cewa babban ɓangaren rikicin Congo yana da alaƙa da ƙasashen waje, kuma nasarar yarjejeniyar zaman lafiyar za ta dogara ne kan kyakkyawar niyya daga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin.
Ya ce: "Ina godiya ga shawarar Shugaba Trump. A gaskiya, ko da yarjejeniyar ba ta yi aiki ba, ba na ganin ya kamata a zargi Amurka saboda a ƙarshe, ba su ne za su aiwatar da abin da muka amince da shi ba. Aikinmu ne, mu a yankin, DRC ko Rwanda, mu aiwatar da ɓangarenmu na yarjejeniyar."
Shekaru da dama na tashin hankali
Ministar Harkokin Wajen DRC, Therese Kayikwamba, ta shaida wa manema labarai a Kinshasa ranar Alhamis cewa gwamnatinta za ta ci gaba da ƙoƙarin ganin an juya yarjejeniyar zuwa zaman lafiya mai ɗorewa, da ci gaban da zai ɗore, da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a lardunan gabashi da kuma faɗin yankin gaba ɗaya.
Gwamnatin DRC da ƙungiyar M23 sun bayyana a ranar Alhamis cewa za su tura wakilai zuwa Qatar don ci gaba da tattaunawa da nufin kawo ƙarshen rikicin.
Gabashin DRC ya sha fama da tashin hankali tsawon shekaru da dama.
Sake ɓullar ƙungiyar 'yan tawaye ta M23 a shekarar 2021 ya ƙara tsananta rikicin.
Fada tsakanin M23 da sojojin gwamnatin DRC a gabashin Congo ya tilasta wa mutane akalla 500,000 yin gudun hijira kuma ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 3,000 zuwa ƙarshen watan Fabrairu, a cewar Cibiyar Nazarin Tsare-tsare ta Afirka.