GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Rundunar Qassam ta yi nasarar kashe sojojin Isra'ila biyar duk da luguden wutar da ake mata
Bisa bayanan rundunar sojin Israila, yawan sojojinta da aka kashe tun farkon yakin Gaza ya kai 888.
Rundunar Qassam ta yi nasarar kashe sojojin Isra'ila biyar duk da luguden wutar da ake mata
Five Israeli soldiers killed in Gaza. / AA
8 Yuli 2025

Kungiyar Qassam Brigades, reshen sojojin Hamas, ta dauki alhakin kashe sojojin Isra'ila guda biyar a ranar 7 ga watan Yuli.

Abu Obaida, mai magana da yawun Qassam Brigades, ya bayyana cewa, “aikin Beit Hanoon mai rikitarwa” da mayakan suka gudanar a ranar Litinin ya zama “wani lamari da ya girgiza martabar sojojin Isra'ila,” tare da yin barazanar “kama ƙarin sojoji” nan gaba.

Ya kara da cewa, “Ko da yake rundunar sojin Isra'ila ta samu nasarar ceto sojojinta daga bala’in, suna iya kasa yin hakan nan gaba, wanda zai haifar da karin fursunoni a hannunmu.”

Ya ce, “Juriya da karfin hali na Falasdinawa da jarumtar ‘yan gwagwarmaya suna tsara yadda mataki na gaba zai kasance,” yana mai cewa, “mummunan kuskuren da Firaminista Benjamin Netanyahu zai iya yi shi ne barin sojojinsa a cikin Gaza.”

Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne lokacin da wata tawagar sojoji daga Netzah Yehuda Battalion ke tsallaka garin Beit Hanoon.

“Yayin da ake kwashe wadanda suka jikkata daga wurin fashewar, wasu ‘yan bindiga sun bude wuta daga wani kwanton-bauna kan sojojin da ke aikin ceto, wanda ya haifar da karin asarar rayuka,” in ji gidan rediyon.

Isra'ila ta yi luguden wuta tare da lalata kusan dukkan Gaza, inda ta kashe fiye da mutum 57,000, yawancinsu fararen hula.

Duk da lalata yankin Falasdinawa da rusa shi, mayakan gwagwarmaya sun ci gaba da kai hare-hare kan sojojin Isra'ila a kasa.

Isra'ila ta yi ikirarin kashe dubban mayakan Hamas. Sai dai masu fafutuka na kare hakkin ɗan’adam suna da shakku kan alkaluman da Tel Aviv ke bayarwa, kasancewar sojojin Isra'ila sau da yawa suna kashe mutanen da ba su dauke da makamai suna masu cewa mayaƙa ne.

A ranar 6 ga watan Yuni, sojojin Isra'ila hudu sun mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a lokacin da wani bam ya fashe a unguwar Bani Suheila da ke kudancin Gaza.

A ranar 25 ga watan Yuni, sojojin Isra'ila bakwai sun mutu a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza lokacin da wata mota mai sulke ta ci karo da wani abu mai fashewa, in ji Tel Aviv.

A cewar bayanan sojojin Isra'ila, adadin sojojin da suka mutu tun farkon yakin Gaza ya kai 888, ciki har da 444 da suka mutu yayin farmakin ƙasa da aka fara a ranar 27 ga watan Oktoban 2023.

Aƙalla sojoji 6,060 sun jikkata, ciki har da 2,768 da suka samu rauni yayin farmakin ƙasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us