Faransa ta fara mika sansanonin soja a Senegal a ranar Juma’a a wani bangare na janye sojojinta daga kasar ta Yammacin Afirka, sansanonin da aka kafa tun 1960.
Ofishin jakadanci Faransa a Dakar ya sanar da cewa an mika wurare da gidaje a yankunan Marechal da Saint-Exupery na Dakar ga hannun gwamnatin Senegal.
Sauran kuma “za a mika su ne kamar yadda bangarorin biyu suka amince da jadawalin da suka sanya wa hannu”, kamar yadda ya fada ba tare da bayanin lokutan da aka zayyana ba.
A ranar 12 ga Fabrairu Faransa ta sanar cewa ta kafa wani kwamiti na hadin gwiwa da Senegal da zai shirya tsare-tsaren ficewar sojojin Faransa da kuma mika sansanonin zuwa karshen shekarar nan.
‘Garen-bawul ga hadaka ’
Ofishin jakadancin ya ce kwamitin ya zauna a karon farko a ranar 28 ga Fabrairu.
“Kwamitin ya kuma kaddamar da aikin yin garen-bawul ga hadakar tsaro,” a cewar sanarwar.
Senegal ta samu ‘yancin kanta daga Faransa a 1960, amma ta kasance daya daga mafiya kusanci da tsohuwar wacce ta yi mata mulkin mallaka a Yammacin Afirka.
Sai dai bayan zaben da aka yi a 2024, gwamnatin Senegal ta yi alkawarin yin mu’amala da Faransa daidai yadda take mu’amala da abokan hulda na waje.
Sanar da janyewa
A watan Nuwamba ne Shugaba Bassirou Diomaye Faye wanda ya lashe zabe bisa akidar kawo sauyi, ya bayyana cewa duka sojojin Faransa da na kasashen waje za su fita daga Senegal zuwa karshen 2025.
‘Yan Senegal da ke yi wa sojojin Faransa aiki za su rasa ayyukansu ranar 1 ga watan Yuli, kamar yadda kwamandan sojojin ya rubuta a wata takarda da ya aike wa shugaban ma’aikatan ‘yan Senegal.
Mutane 162 ne ke aiki kai tsaye a sansanonin sojojin Faransa a Dakar da yankunan da ke kusa da birnin, yayin da kimanin mutane 400 zuwa 500 suke aiki ta hannun wasu kamfanonin da ke yi wa sojojin kwangila.
Sojojin Faransa sun gudanar da wani zama na musamman a ranar Alhamis don ba da “damar sauyin wuraren aiki” ga ma’aikatan 162 da za su rasa ayyukansu.