AFIRKA
12 minti karatu
Ɓoyayyun Dauloli: Bayyana ɓoyayyun labaran Afrika da kuma tabbatattun fasahohi
Mulkin mallaka ba ya sace ma'adanan Afrika ba ne kawai, har ma tunaninta ya yi yi awun gaba da shi. Wannan kawarwan ya bar tabo.
Ɓoyayyun Dauloli: Bayyana ɓoyayyun labaran Afrika da kuma tabbatattun fasahohi
Mansa Musa (circa 1280-circa 1337) / Getty Images
29 Maris 2025

Daga Dwomoh-Doyen Benjamin

Tsawon ɗaruruwan shekaru, labarin Afrika yana fitowa ne daga bakin waɗanda ba ƴan nahiyar ba - an taƙaita ƙasaitaccen tarihinta zuwa mulkin mallaka, ana kuskuren ɗaukar arziƙinta a matsayin talauci, kuma ala'umarta, a galibin lokaci, ana kallon ta a matsayin mai fafutika a maimakon wacce ta yi nasara.

A ƙarƙashin waɗannan shimfiɗun akwai wata nahiya cike da ɗimbin ɓoyayyun labarai da kuma tabbatattun fasahohi, ƙasa inda masarautu suka taɓa wanzuwa a matsayin kogin ilimi, da iko da kuma fasaha.

A yau, ƙalubalen da ke gabanmu ba kawai mu tuna da waɗannan tarihin ba ne face mu sake nazarin su - domin mu sake gano asalinmu ta rayuwar magabatanmu sannan mu shata hanyar da za ta sake bayyana yadda duniya ke kallon Afrika, da kuma mafi muhimmanci, yadda ƴan Afrika da kansu ke kallon junansu.

Ta hanyar bayyana basirar waɗanda suka gabace mu, ƴan Afrika za su iya kawar da kuɗin goro da ake musu, kuma su gina wata duniya, inda ake kallon nahiyar a matsayin wacce ake tunawa da ita, ba a matsayin "mai tasowa" ba.

Asalin abin da ya kawo ruɗani 

Bari mu fara da gaskiyar da ba kasafai ake faɗin ta ba: Afrika ita ce asalin wacce ta fara haddasa ruɗani. Yi duba da daular Aksum, da ta ƙunshi Ethiopia da Eritrea na wannan zamanin.

 Zuwa ƙarni na 4th, al'ummar Aksumawa suna sassaƙa dutse mai tsawon taku-90 daga manyan duwatsu - ba tare da amfani da wata na'ura ba.

Kuɗaɗensu na ƙarfe,ɗauke da tambarin fuskokin sarakuna, sun zazzaga daga Rome zuwa Indiya. Ba su jira wasu daga waje su nuna musu ɗaukaka ba;sun gina shi.

 Sannan akwai Daular Mali. Lokacin da Mensa Musa ya yi tattaki zuwa Makka a shekarar 1324, tawagarsa ba ɗauke da zinariya kaɗai take ba; tana ɗauke da iko da ƙasaita. Masana tarihi sun ce hidimar da ya yi a Alƙahira ta karya farashin zinariya na tsawon shekara goma.

Amma arziƙin Mali na asali shi ne Timbuktu,inda masana suka rubuta dubban littattafai kan Shari'a, ilimin taurari da kiwon lafiya. Waɗannan ba tarin takardu ba ne, manufofin kawo sauyi ne.

Wata maƙalar Timbuktu ta ƙarni na 15th kan zazzaɓin cizon sauro, ta buƙaci likitoci da "su saurari numfashin majinyaci, ba na ababan bauta ba kaɗai," suna ƙalubalantar camfe camfen zamanin.

Wani hoton Mensa Musa,Sarkin Mali a wata taswirar Afrika ta Arewa 1375

A kudancin Afirka, mashahuriyar katangar dutse zalla da ba yi amfani da kwaɓaɓɓiyar ƙasa ba ta Zimbabwe - ta zarci tunani.

Tsawon shekaru 300, wannan birnin na bunƙasa kan kasuwanci da noma, ala'umarsa na noma dawa a ƙasar da ke fama da fari, suna amfani da dabarun da masana aikin gona har yanzu suna nazari a kai. 

Magabatanmu wayayyun ƴan Afrika ne da ke ƙere ƙeren abubuwan ban mamaki.

 Tunanin da aka sace

Mulkin mallaka ba sace arziƙin Afrika kaɗai ya yi ba,har tunaninta ya yi awun gaba da shi.

Wani kakana Allah ya ji ƙansa, ya taɓa gaya mini cewa makarantun Turawan Birtaniya sun sanar da shi cewa tarihinsa ya fara ne daga shekarar 1471, "lokacin da ƴan Portugal suka iso."

Ba da taɓa ambaton sunan Sarauniya Amanirenas ( 60 BC- 10 BC), jarumar sarauniyar daular Kush wacce ta jagoranci mutanenta suka bijirewa mamayar Romawa, ko kuma ƙasaitaccen - Gunkin Tagulla na Benin da aka narka aka sake masa fasali, ko kuma rayuwa a Ille Ife da kuma hijirar ƴan Afrika domin mamaye wuraren da babu masu su.

Wannan kawarwar ya bar tabo

Bara a Kampala, na gamu da wani mai gina manhajar komfuta ɗan shekaru 19 da haihuwa, wanda ya tabbatar min cewa bai taɓa jin labarin daɗaɗɗen tsarin ban-ruwa na mutanen Massai ba.

 "A maimakon haka, sai suka koya mana tsarin ban-ruwa na Romawa," ya gyaɗa kai.

Idan aka gaya maka kakaninka ba wayayyu ba ne, sai ka fara shakkun basirar da kake da ita.

Amma da daɗewa kafin hulɗa da Turawa, daular Benin (Nijeriya a wannan zamani) ta ƙaddamar da aikin ƙasa na Benin, wasu jerin katangu da tonannun ramuka masu tsawon fiye da kilomita 16,000 -  tsawon da ya fi na Mashahuriyar Katangar China (Great Wall of China).

Waɗannan gine gine, waɗanda aka gina su tsakanin ƙarnin - 800 - 1400, sun bayar da kariya ga biranen masu sana'o'in hannu, masu ilimin taurari da kuma masu shata dokoki da ke bunƙasa.

Farantai da aka ƙera da ma'adanin brass, waɗanda Turawan Birtaniya da suka yi mulkin mallaka a shekarar 1897 suka sace, ya bayyana al'umma wacce mata ke riƙe da iko na Shari'a da kuma dabarun sarrafa ƙarafa.

A yanzu, mai zanen gine-gine ɗan Nijeriya, Olajumoke Adenowo yana kwaikwayon waɗannan tsare-tsaren, da gauraya salo daga aikin fasaha na Benin zuwa samar da gidaje marasa yi wa muhalli lahani.

Daga nan kuma, daga Mogadishu zuwa Sofala, birane - ƙasashen Swahili kamar Kilwa (Tanzania) da Gedi (Kenya) suna samun bunƙasa a harkar kasuwanci da diflomasiyya da kuma fasaha.

Fadar Husuni Kubwa ta Kilwa tana da bayan gida irin na wannan zamanin da ake sarrafa ruwa ta bututu a ƙarni na 13th. Tsarin ginin nasa yana kama da gidajen zamani na Tsibirin Lamu. 

A yanzu, Cibiyar Fasaha ta Mombasa ta yi aro ne daga ƴan garanci irin Swahili:Harkoki kamar Ushahidi ("sheda" a harshen Swahili) suna amfani da manhaja su zana taswirar tashe tashen hankali a duniya kamar yadda ƴan kasuwar Swahili a da suka yi taswirar guguwar Monsoon.

Sarakunan Kushite na Sudan sun mulki Masar na tsawon ƙarni ɗaya (744 - 656 BCE), suka gina pyramid fiye da maƙwabtansu na kudanci.

Sarauniya Amanirenas ta yi galaba kan dakarun Romawa a shekarar 24 BCE, ta ƙulla wata ƴarjejeniyar da ta tsame mutanenta daga biyan hadaya.

Ƴar gwagwarmayar Sudan ta wannan zamanin ta yi misali da ita a matsayin alama ta bijirewa yayin juyin juya halin shekarar 2019.

 Ƙarin bayani

Har wa yau, a daidai shekarar 1500 BCE, al'ummar Nok na tsakiyar Nijeriya sun ƙagi mutum mutumin ƙonanniyar laka a zahirance, ta kai ga matsayi a al'ummance, yanayin kitso, har ma da harkokin kiwon lafiya sun bayyana.

Fasaharsu daga bisani ta yi tasiri kan al'adun Yarbawa da Ibo. Yanzu, masu aikin zane zane na Lagos kamar Laolu Senbanjo (“The Sacred Art of the Ori”) sun farfaɗo da fasahar ta Nok, ta hanyar amfani da zanen fenti da hoto domin nuna adawa da cin hanci da rashawar siyasa.

Ƙabilar Asante na Ghana (1701 - 1957) ta yi mulki a irin tsari na sarauta mulkiyya ta je-ka-na-yi-ka, inda ƴan'ƙasa za su iya tsige lalatattun shugabanni.

Suturarsu ta Kente, da aka saƙa da alamu na haɗin kai da adalci, ta zama wata alama ta kishin - Afrika.

A yanzu, gangamin Ghana na "Shekarar Dawowa" ("Year of Return"),da kuma shirin ƴan Afrika mazauna ƙasashen waje na sake fasalin shirye shiryen ƴan Afrika mazauna ƙasashen waje domin ya dace da buƙatun Afrika -  (Re-Africanization of the Diaspora programs) wanda ke sake haɗe ƴan Afrika mazauna ƙasashen waje da tushensu - sun yi amfani da salon Kente tallata kansu, alamar amincewa da shugabanci na magabata.

Gunkin tagulla na Benin kenan a akwatin baje-koli a gidan ajiye kayan tarihi na Rautenstrauch-Joest Museum.

Wannan ya koma da mu can baya cikin Saharar Libya, inda ƴan ƙabilar Garamantes (500 BCE - 700 CE) suka yi gini ya bi ta kan wani magudanar ruwa na ƙarƙashin ƙasa da ake kira forggaras.

Waɗannan mashigan ruwan, wasunsu masu tsawon kilomita 50, sun zamar da shaharar ta zama waje mai dausayi.

Manoman Sahara na zamani, da ke fama da sauyin yanayi, suna farfaɗo da waɗannan hanyoyin domin magance fari.

A Agadez, Nijar, injiniyoyi suna amfani da hoton tauraron ɗan'adam domin shata foggaras na zamanin baya - sheda da ke nuna cewa yankin da ya fi ko ina rashin dausayi a Afrika, a baya, ya samar da abincin da miliyoyin mutane suka rayu da shi.

Sirkakken gado

Ɓoyayyun daulolin Afrika ba su taɓa kasance a kaɗaice ba.Hijirar Bantu (3000 BCE - 500 CE), masu asali daga Cameroon, sun yaɗa aikin ƙarafa da harshen a cikin ƙasashen Afrika 20.

Yanzu, ƴan Afrika mutum miliyan 350 suna amfani da harsunan Bantu. A Johannesburg, ma'aikaciyar jinya mai amfani da harshen Xhosa da kuma injiniya mai amfani da harshen Kikuyu za su iya yin muhawara kan siyasa, ba tare da sanin magabatansu ne suka haɗa kai wajen ƙago kayayyakin amfani na ƙarfe na farko ba.

Hijirar Mfecane ta daular Zulu ta ƙarni na 19th ta sake fasalin Afrika ta Kudu, ta tarwatsa al'umomin Sotho, da Ndebele da kuma Swazi.

Ƙasar Afrika ta Kudu ta wannan zamanin "Launin Bakan Gizo" ya siffantu da wannan sirkakken gadon. Lokacin da gwanar girke girke ta Cape Town Nthati Moshesh ta girka abincin ƙabilar Zulu, umleqwa tare da dabgen Malay, tana jaddada haɗin kai wajen girki ne, wanda hijira da aka yi a zamanin baya ta haifar.

 Hatta waɗanda aka bautar suna ɗauke da dauloli a ɓargonsu.

A Bahia, Brazil, magabatan ƙabilar Yarbawa da suka fito daga Ille Ife har yanzu suna naɗa sarauniya Ayaba (Uwar sarauniyoyi) domin adana dodon Egungun.

Malamin addinin Vodou a ƙasar Haiti yana kira da neman taimakon kuruwoyin jaruman daular Dahomey yayin zanga-zanga.

A yanzu, Accompong Maroons na Jamaica, suna bukin gadonsu na Akan a bukin shekara shekara da ya haɗa da kaɗe kaɗe da kuma wasu surkulle na martaba magabatansu kamar Nanny.

A Suriname, ƙabilar Ndyuka suna amfani da sunayen Akan - Kwasi (Lahadi) ko Afia (Juma'a)-suna kiyaye wani tsarin kwanan wata daga magabatansu.

Hatta lafazin"kai kai" (a tattauna) a harshen Trinidad, ya bayyana lafazin Koko (yi magana) na Akan.

Waɗannan mazauna ƙasashen wajen sheda ce ta zahiri: Daulolin Afrika ba su taɓa watsewa ba - sun ninninka ne.

Yayin da ƴar gwagwarmayar kare muhalli ƴar Uganda, Vanessa Nakate ta yi jawabi a gaban Babban Taron MDD, ta ambaci dokokin gudanarwa na daular Buganda -na ƙarni na 18th.

Yayin da Edna Adan Ismail ta gina asibititocin karɓar haihuwa, ta bayar da misali da unguwarzoma aWhen Ugandan climate activist Vanessa Nakate speaks at U.N. summits, she invokes Buganda Kingdom’s 18th-century land stewardship laws.

Lokacin da Edna Adan Ismail ta Somaliland ta gina asibitocin karɓar haihuwa, ta bayar da misali da unguwazoma na zamanin daular Adal Sultanate.

Bayyana gaskiya

Waɗannan matan ba suna martaba tarihi ba ne kaɗai, suna bayyana gaskiya ce: Ƙasashen Afrika guda 54 rassan bishiya guda ne.

Daular Kongo (1390 - 1914) ta ƙunshi Angola, da Congo, da Gabon. A yanzu, waɗannan ƙasashen suna amfani da harshen Kikongo da tsarin haula iri ɗaya.

Lokacin da mai waƙar gambara ɗan ƙasar Angola Ikonoklasta ya ɗan ambaci sassaƙar dutse a waƙarsa, yana gaya wa ƴan zamaninsa: "Iyakokinmu na bogi ne Jininmu na gaske ne."

Hatta sauyin yanayi ana kan magance shi da basirar magabata. A Nijar mai fama da fari, manoma sun farfaɗo da dabarun zai - binne ruɓaɓɓun tsirrai domin tare ruwan sama, hanyar da kakanninsu suka yi amfani da shi.

Amfanin gona na ninkawa."Ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba na Turawa suna ci gaba da buƙatar yin nomar rani mai cin kuɗi," wani manomi ya sheda mani. "Amma ruɓaɓɓun tsirranmu na tare da bayan buƙatar.

Wannan ba faɗan Afrika ba ne kaɗai. Lokacin da mai zanen gine gine ɗan Burkina faso, Diébédo Francis Kéré ya lashe kyautar  the Pritzker Prize (kyautar zanen gine gine), ya ce ɗakin laka na kakansa ne ya koya masa tsarin gini mai wadatacciyar iska.

Yanzu, makarantunsa na koyar da gini da laka da ke Jamus da Kenya manuniya ne ga yadda ake rayuwa mai ɗorewar.

Ko kuma duba Masi Mamombe,mai gwagwarmaya ɗan ƙasar Zimbabwe, wanda ya ambato abin da Nehandar Nyakasikana-shugaban addini wanda ƴan mulkin mallaka suka rataye a shekarar 1898- lokacin da ake gudanar da zanga-zanga.

Nehanda ba ta mutu ba domin mu roƙi demokradiyya ba, Mamombe ta sheda mini."Ta mutu ne saboda mu tuna da ikonmu."

Tunawa da iko

Zan bar ka da wani labari da ba zan iya mantawa da shi ba.A wata unguwar marasa galihu ta Nairobi, gungun wasu matasa suka sace wata lalatacciyar na'urar majigi da ake nuna fim kan ƴan tawayen Mau Mau.

Daga baya, sai suka yi muhawara kan yadda za su buɗe wata manhajar ƴancin mallakar ƙasa. Wata yarinya ta ce, "idan Wangu wa Makeri zai iya jagorantar Kikuyu a 1900, me ya sa ba zan iya jagorantar tawagar fasaha ba"?

Tsawon lokaci, masu son kwasar dukiyar Afrika yayin da kuma suke watsi da basirarta, su suke rubuta labarai kan Afrika. Amma yanzu wannan zamanin na kawo wa ƙarshe.

Alhakin yanzu yana wuyan ƴan Afrika - musamman matasa - su dinga bayar da tarihinsu sannan su shata makomarsu.

Hakan na nufin yin watsi da tunanin cewa wahalhalun Afrika su ke bayyana ta sannan kuma, a maimakon rungumar gaskiyar cewa nahiya ce masu sarrafawa, masu zurfin tunani kuma shugabanni.

Yaya za a cim ma hakan? Ilimi jigo ne.Wajibi makarantu a faɗin Afrika su saka tsarin ilimin gida a manhajarsu, suna jinjina wa tarihin Afrika a matsayin jigon labari.

Fasaha dole ita ma ta taka rawa - finafinai,adabi da kuma kaɗe kaɗe dole ne a dinga samo su daga ayyukan gwarazan Afrika, domin tabbatar da cewa masu tasowa na kallon kansu tsundum a labaran nasu da kansu.

Dole harkokin kasuwanci su zuba jari a baiwar da ake da ita a cikin gida, mu gane cewa masalaha ga ƙalubalen Afrika tana nan a cikin gida,ba a waje ba.

Wajibi ne su ma shugabannin Afrika su gano cewa ƴancin cin gashin kai ba siyasa ba ce kaɗai, al'ada ce, kaifin ilimi ne sannan tattalin arziƙi ne.

Ƙwato gurbin Afrika a matakin duniya na buƙatar gusawa daga dogaro da wani zuwa dogaro da kai, daga mai neman tallafi daga ƙasashen duniya zuwa ƙalla muhimman ƙawance, da kuma daga tsarin neman bashi zuwa tsarin da aka ƙirƙire shi a nan gida da yake mutunta al'adun da ɗabi'un Afrika.

Duniya ta zuba ido, amma abu mafi muhimmanci, ƴan Afrika na farkawa.

Lokaci ya yi da za a bayyana ɓoyayyun dauloli, a faɗi ɓoyayyun labarai, sannan tare da ƙasaita, mu tunkari makomarmu da take martaba gadon da magabatanmu suka bar mana, yayin da kuma muke shata sabon babi ga masu zuwa nan gaba.

Marubucin, Amb Dwomoh-Doyen Benjamin,shi ne daraktan gudanarwa na cibiyar masu shirye shirye ta Afrika

Togaciya: Ra'ayoyi da marubucin nan ya bayyana ba dole ba ne su zo daidai da ra'ayi, hange ko manufofin editan TRT Afrika ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us