AFIRKA
2 minti karatu
Rwanda ta fice daga ƙungiyar ECCAS kan rikicinta da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
Rwanda ta sanar da ficewarta daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Tsakiyar Afirka (ECCAS), in da take zargin Jamhuriyar Kongo da yi mata bi-ta-da-ƙulli da tauye mata haƙƙoƙinta tare da goyon bayan wasu ƙasashe mambobi.
Rwanda ta fice daga ƙungiyar ECCAS kan rikicinta da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
Rahotanni sun ce ƙoƙarin da hukumomi suka yi a baya don rage rikici tsakanin Kinshasa da Kigali a tarurrukan sirri a gefen taron ƙoli ya ci tura. / Reuters
8 Yuni 2025

Kasar Rwanda ta sanar da ficewarta daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Tsakiyar Afirka (ECCAS), inda take zargin maƙwabciyarta Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da “amfani da kungiyar” tare da goyon bayan wasu kasashe mambobi.

“Hakkin Rwanda na shugabancin karɓa-karɓa kamar yadda aka tanada a Sashe na 6 na yarjejeniyar kafa ECCAS, an yi watsi da shi da gangan” bisa umarnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Rwanda a ranar Asabar.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an ware Rwanda daga taron koli na 22 na ECCAS da aka gudanar a Kinshasa a shekarar 2023 karkashin jagorancin Kongo, yayin da rikici tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tsananta.

Gwamnatin Rwanda ta jaddada cewa wannan yanayin wata sabuwar shaida ce ta “wuce gona da iri” na ƙungiyar, kuma ba ta wani dalili na ci gaba da kasancewa mamba na wata ƙungiya da ke aiki ba bisa ka’idoji da amfanin da aka kafa ta ba.

Naɗin sabon shugaban ECCAS, wanda aka shirya yi a taron koli na ranar Asabar, an ɗage shi bayan rahotanni sun nuna cewa Kongo ta ƙi amincewa da miƙa shugabancin daga Equatorial Guinea zuwa Rwanda a wani mataki na karɓa-karɓa.

Yunƙurin sulhu da ba yi nasara ba

Matakin da Kigali ta ɗauka a karshen taron ƙoli na 26 da aka gudanar a Malabo dake Equatorial Guinea, yana nuna karuwar rikici tsakanin Rwanda da Kongo dangane da rikicin da ke gabashin Kongo.

Rahotanni sun ce ƙoƙarin da hukumomi suka yi a baya don rage rikici tsakanin Kinshasa da Kigali a tarurrukan sirri a gefen taron ƙoli ya ci tura.

Firaministan Rwanda, Edouard Ngirente, ya halarci taron ƙolin.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo tana zargin Rwanda da goyon bayan ‘yan tawayen M23 da ke yaƙi a gabashin Kongo, wanda Kigali ta musanta.

ECCAS ta soki ƙungiyar ‘yan tawaye tare da kiran a “gaggauta janye sojojin Rwanda daga yankin Kongo.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us