KASUWANCI
2 minti karatu
Buhun gero ya kai kimanin Cefa 30,000 a Nijar, in ji SIMA
Kamfanin dillancin labaran Nijar ya alaƙanta tashin farashin na gero da bikin Tabaski inda ake yawan sayen gero a birane da ƙauyukan ƙasar.
Buhun gero ya kai kimanin Cefa 30,000 a Nijar, in ji SIMA
Gero na cikin ababen da aka fi nomawa a Nijar / Getty Images
10 Yuni 2025

Farashin gero na ƙaruwa a kasuwannin kayayyakin abinci a ƙasar Nijar, yayin  da farashin sauran hatsi ke ci gaba da kasancewa yadda suke a baya, kamar yadda alƙaluman da ofishin ba da bayanai game da kasuwar kayayyakin abinci (SIMA) na ƙasar ya fitar.

Alƙaluman na makon da ke tsakanin ranar Laraba 28 ga watan Mayu zuwa ranar Talata 3 ga watan Yunin shekarar 2025 sun nuna cewa farashin gero ya ƙaru da kashi 1 cikin 100 daga 28,860 FCFA zuwa 29,052 FCFA, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar, ANP.

Rahoton na ANP ya ce hakan ya faru ne duk da wadatar kayan abincin a kasuwa saboda buƙatar bikin Tabaski da ake yi ranar 6 ga watan Yuni.

“Idan aka kwatanta da lokaci mai kaman haka a shekarar da ta gabata (2024), farashin ya ragu da kashi 20 cikin 100, yayin da ya ɗara matsakaicin farashi na shekara biyar da suka wuce (2020–2024) da kashi 2 cikin 100,” in ji rahoton na ANP.

Kazalika rahoton ya ce akwai muhimmin saɓani a farashin hatsin a wurare daban-daban inda ake samun buhun kan farashi  21,131 FCFA a N'Guelkolo, lamarin da ke nuna samuwarsa kuma tsadarsa ke kai 45,000 FCFA a Iférouane, inda yake da wuyar samuwa sosai.

“A birnin Yamai, farashin buhun gero mai nauyin kilogiram 100 ya ƙru da kashi 4 cikin 100 idan aka kwatanta da makon da ya gabata. A yanzu ana sayarwa ne kan kuɗi 28,000 zuwa 29,000 FCFA, dangane da kasuwa ko kuma nau’in geron,” in ji ANP.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya alaƙtanta tashin farashin na gero da bikin Tabaski inda ke yawan sayen gero a birane da ƙauyukan ƙasar.

Saɓanin farashin gero, ana sayar da buhun dawa mai nauyin kilogiram 100 kusan kamar yadda yake a makon da ya gabata ne inda a da ake sayar da ta 25,738 FCFA , kuma a yanzu ake sayar da buhunta 25,866 FCFA in ji ANP.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us