Amurka da Isra'ila sun samu saɓani kan kusancin Iran da ƙera makamin nukiliya, inda rahotannin leƙen asirin Amurka ke nuna cewa Tehran za ta kai shekaru biyu zuwa uku kafin ta cim ma wannan burin, yayin da Tel Aviv ke jaddada cewa barazanar a kusa take sosai, kamar yadda rahotannin manema labarai suka bayyana a ranar Talata.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi iƙirarin cewa Iran tana gaggawar ƙera makamin nukiliya, wanda ya sa Isra'ila ta kai hare-hare kan gine-ginen nukiliya da na sojojin Iran, kamar yadda CNN ta ruwaito.
Sai dai, wasu majiyoyi hudu da suke da masaniya kan batun sun shaida wa CNN cewa hukumomin leƙen asirin Amurka ba sa ganin cewa Iran tana kera makamin nukiliya a halin yanzu, kuma suna kiyasta cewa za a ɗauki a ƙalla shekaru biyu zuwa uku kafin ta iya samarwa da amfani da irin wannan makamin.
Hare-haren da aka kai kwanan nan sun lalata wasu gine-ginen nukiliya kamar Natanz, amma sun bar cibiyar Fordow wacce take da tsananin tsaro ba tare da wata illa ba.
Masana tsaro sun ce, idan har ana so a lalata cibiyar Fordow, Isra'ila tana bukatar wasu makamai na musamman daga Amurka da kuma tallafin jiragen sama, kamar yadda rahoton ya bayyana.
“Isra'ila na iya kai hare-hare kan wadannan gine-gine na nukiliya, ta hana su aiki, amma idan ana son a lalata su gaba daya, dole ne ko dai sojan Amurka su kai hari ko kuma a cim ma wata yarjejeniya,” in ji Brett McGurk.
Trump ‘bai damu‘ da abin da hukumomin leken asiri suka ce ba
Bambancin nazarorin da aka yi sun jefa gwamnatin Trump cikin tsaka mai wuya, wadda ke kokarin kauce wa rikici yayin da take shirin daukar matakan ramuwar gayya.
Daraktan Leken Asiri na Ƙasa, Tulsi Gabbar, ya bayyana a farkon watan Maris cewa hukumar leƙen asiri ta gamsu cewa Iran ba ta ƙera makamin nukiliya.
Trump ya yi watsi da wannan bayani na Gabbar, yana cewa, “Ba na damu da abin da ta faɗa ba — ina ganin suna kusa sosai su samur da makamin.”
Tashin hankali a yankin ya ƙaru tun ranar Juma’a, lokacin da Isra'ila ta kai hare-hare ta sama kan wurare da dama a Iran, ciki har da gine-ginen sojoji da na nukiliya, wanda ya sa Tehran ta kai hare-haren ramuwar gayya.
Hukumomin Isra'ila sun ce aƙalla mutane 24 sun mutu kuma daruruwan sun jikkata a hare-haren makamai masu linzami na Iran tun daga lokacin.
Iran ta ce akalla mutane 224 sun mutu kuma sama da 1,000 sun jikkata a harin da Isra'ila ta kai.