AFIRKA
2 minti karatu
Ɗaruruwan mutane ne suka mutu a hare-haren satar dabbobi a Kudancin Sudan
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashe-kashen sun faru ne a cikin wata biyun da suka gabata sakamakon ta'azzarar rikice-rikicen ƙabilanci.
Ɗaruruwan mutane ne suka mutu a hare-haren satar dabbobi a Kudancin Sudan
South Sudan has seen years of violence including communal clashes. / AP
3 Yuni 2025

Daruruwan mutane sun mutu tun watan Disamba sakamakon rikicin kabilanci da ke kara tsananta a Sudan ta Kudu, wanda aka alakanta da satar shanu da hare-haren ramuwar gayya, in ji Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata.

Faɗan da ake yi kan samun damar amfani da albarkatun kasa da kuma satar shanu ya zama ruwan dare a kasar, wadda ke fama da matsanancin fari da ambaliyar ruwa.

Rikicin tsakanin makiyaya ya zama ruwan dare a Tonj East, da ke cikin jihar Warrap a arewa maso yammacin Sudan ta Kudu, inda aka samu "mutuwar ɗaruruwan mutane, lalata gidaje da kuma raba mutane da muhallansu," a cewar Hukumar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu (UNMISS).

“A watan Maris, an ƙiyasta cewa fiye da mutum 200 sun mutu a rikicin ƙabilanci,” in ji UNMISS a cikin wata sanarwa.

Rikicin Siyasa

“Ana bukatar daukar mataki cikin gaggawa daga gwamnatin kasa don hana rikicin kai wa ga matakin da ba za a iya shawo kansa ba, tare da haɗo kan al’ummomi don warware matsalolin cikin lumana,” in ji Guang Cong, mataimakin wakilin musamman na UNMISS.

A watan Fabrairu, wani jami'in yankin ya yi tir da abin da ya kira “kisan gilla” a jihar Eastern Equatoria da ke kudu, inda aka kashe mutane 41 ciki har da mata da yara, aka raunata 65, sannan da dama suka ɓata, a cewar sanarwar.

Irin wadannan rikice-rikicen na cikin gida sun ƙara tsananta matsalar da Sudan ta Kudu ke fuskanta, wadda ta sha fama da rashin kwanciyar hankali na siyasa da rikicin kabilanci tun bayan samun 'yancin kai daga Sudan a shekarar 2011.

Kasar ta kuma fuskanci watanni na rikice-rikicen cikin gida tsakanin dakarun da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir da abokin hamayyarsa na dogon lokaci, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko, Riek Machar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us