AFIRKA
1 minti karatu
Hukumomin Aljeriya sun kori dubban 'yan Nijar daga ƙasar
Gidan talbijin na gwamnatin Nijar RTN ya ruwaito cewa gwamnatin Aljeriya ta kori dubban mutane, ciki har da mata da ƙananan yara tun daga farkon watan Afrilu.
Hukumomin Aljeriya sun kori dubban 'yan Nijar daga ƙasar / TRT Afrika Hausa
25 Afrilu 2025

Hukumomi sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin Aljeriya ta kori dubban 'yan ƙasar Jamhuriyar Nijar da ma 'ya'yan wasu ƙasashen Afirka daga ƙasar, suna masu bayyana hakan a matsayin karya dokar ƙasashen duniya.

Gidan talbijin na gwamnatin Nijar RTN ya ruwaito cewa gwamnatin Aljeriya ta kori dubban mutane, ciki har da mata da ƙananan yara tun daga farkon watan Afrilu.

Hakan na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da zaman doya da manja tsakanin Aljeriya da ƙasashen AES bayan Mali ta zargi Aljeriya da harbo wani jirginta maras matuƙi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us