DUNIYA
4 minti karatu
Yaya girman gargadin China da ke cewa 'za ta yi faɗa da Amurka iya ƙarfinta'?
Yayin da kasashen China da Amurka ke musayar zafafan kalamai kan karin haraji, ana ci gaba da bayyana irin tasirin da wannan takaddamar za ta haifar ta fuskar tattalin arziki mai tsanani a duniya.
Yaya girman gargadin China da ke cewa 'za ta yi faɗa da Amurka iya ƙarfinta'?
Sai dai masana daga China sun ce duk da wannan sa’insa mai zafi, matsayin hukuma na Beijing bai sauya ba. / AP
7 Maris 2025

Tashin hankalin da ke faruwa a tsakanin China da Amurka a fannin kasuwanci ya sake tsananta, inda musayar zafafan maganganun da sanya haraji mai tsanani suka zama alamar sabon zagaye na rikicin tattalin arzikin.

Wannan ya sa masana ke tambayar ko wannan wani mataki ne na siyasa ko kuma duniya ta shiga cikin cikakken yakin kasuwanci tsakanin manyan ƙasashen biyu masu ƙarfin tattalin arziki.

“Idan yaƙi shi ne abin da Amurka take so, ko na sanya haraji ko kasuwanci ko ma wane iri ne, to mun shirya yin faɗan har sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi,” in ji Ofishin Jakadancin China a Amurka, a wani sakon da ya wallafa a ranar 5 ga Maris a shafin X, yana nakalto daga wata sanarwa ta Ma’aikatar Harkokin Wajen China da aka wallafa rana guda kafin haka.

Wasu masana sun bayyana wannan kalaman na China—musamman game da shirye-shiryen “duk wani irin yaki” da kuma maganar “ganin abin da ya ture wa buzu naɗi”—a matsayin wani mataki mai tsanani da bai taɓa faruwa ba, wanda ke nuna karin matsin lamba daga Beijing a rikicin kasuwanci tsakanin China da Amurka.

Sai dai masana daga China sun ce duk da wannan sa’insa mai zafi, matsayin hukuma na Beijing bai sauya ba.

Henry Huiyao Wang, tsohon mai ba da shawara ga Majalisar Ƙasa ta China, ya yi watsi da ra’ayin cewa martanin da China ta mayar ya nuna wani babban sauyi.

“A’a, ban ga wani sabon abu ba a cikin abin da China ta fada,” in ji shi a hirarsa da TRT World, yana mai nuna cewa harajin ramuwar gayya na China bai kai mataki mai tsanani irin na Amurka ba.

“China ta sanya haraji ne kawai kan nau’ukan kayayyaki 80 zuwa 100, yayin da Amurka ta kara haraji a dukkan nau’ukan kayayyaki.

Saboda haka, ban ga wannan a matsayin matakin ramuwar gayya ba, sai dai wani mataki mai sauki da kuma wata alama daga China,” in ji Wang, wanda shi ne kuma shugaban Cibiyar China a matakin Duniya (CCG) da ke Beijing.

Rorry Daniels, Daraktan Gudanarwa na Asia Society Policy Institute, ta ce matsayin Beijing wani mataki ne na lissafi don karfafa matsayinta na tattaunawa.

“Na yi imani China ta yanke shawarar cewa babu wani amfani a sassauta matsayinta kafin tattaunawa ta fara. Beijing ta duba abubuwan da Shugaba Trump ya fi mayar da hankali a kansu kuma ta yanke shawarar samar da wani matsayi don tattaunawa mai tsauri,” in ji ta ga TRT World daga birnin New York.

Wannan, in ji Daniels, yana fayyace abubuwa game da niyyar haƙon fannin noma na Amurka da kuma amfani da kakkausan harshe yaren tabbatarwa.

A halin yanzu, wasu masana suna gargadin ka da a yi fassarar wannan kalaman na China da yawa.

Julien Chaisse, Farfesa a Jami’ar City University of Hong Kong, ya ce duk da cewa amfani harshe mai tsauri ya yi fice, hakan ba lallai ba ne ya nuna wani babban sauyi daga matsayin da China ta dauka a baya.

“China ta dade tana kallon rikicin kasuwanci da Amurka a matsayin wani bangare na kokarinta na tsayayya da matsin tattalin arziki.

A ganina, hakan bai canza ba,” in ji shi ga TRT World, yana mai nuna cewa duk da cewa kalmar “ture wa buzu naɗi” na iya nuna tsanani, martanin da China ta bayar ya kasance na hankali kuma yana dogara da matakan da Washington za ta dauka.

A ranar 4 ga Maris, Shugaba Trump ya kara haraji na kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin shigo da China, wanda ya kai jimillar harajin da aka sanya cikin wata guda zuwa kashi 20 cikin 100.

A nata martanin, Beijing ta sanar da sabon haraji har zuwa kashi 15 cikin 100 kan wasu muhimman kayayyakin Amurka, ciki har da kaji da alade da wake, da nama, tare da takunkumin fitarwa da kuma karin tsauraran dokoki kan harkokin kasuwanci da kamfanonin Amurka.

Masana sun yi gargadin cewa wannan rikicin zai iya yin tasiri mai tsanani kan bangaren noma na Amurka, wanda shi ne mafi girman fitar da kayayyaki zuwa China.

A baya, irin wannan haraji ya sa masu shigo da kayayyakin China sun karkata zuwa Brazil da Argentina don sayen wake.

A karshe, duk da wannan rikici, masana sun yi imanin cewa akwai yiwuwar tattaunawa don samun mafita.

Amma har yanzu, ana ganin wannan rikici na tattalin arziki yana bukatar kulawa mai kyau daga bangarorin biyu don kauce wa mummunan tasiri kan tattalin arzikin cikin gida.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us