Makamai masu linzami na Iran sun faɗa a wasu wurare a Isra’ila, lamarin da ya janyo gobara tare da lalata wani gini bayan tsarin tsaron saman Isra’ila ya kasa tare harin.
Wasu makamai masu linzamin da aka yi imanin cewa an harbo su ne daga Iran sun sauka a cikin Isra’ila, in ji gidan rediyon rundunar sojin Isra’ila.
Duk da cewa rundunar sojin ba ta bayyana haƙiƙanin inda makaman suka sauka ba, jaridar Israel Hayom Daily ta ba da rahoton cewa aƙalla makamai masu linzami biyu sun faɗi a kusa da Birnin Ƙudus da kuma yankin Sharon kusa da Tel Aviv bisa nazari na farko-farko.
Kafar Channel 12 ta ba da rahoton cewa harin na makamai masu linzami ya lalata wani gini a tsakiyar Isra’ila kuma ‘yan kwana-kwana sun amsa kira [na zuwa inda] motoci 20 suka kama da wuta.
Rahotanni sun ce tarkacen makamai masu linzami sun sauka a wani gini a arewacin Isra’ila, yayin da makamai masu linzami da ke faɗowa da burbuɗinsu sun janyo gobara a fili a wurare da dama.
Tun ranar Juma’a ne dai tashin hankali ya yi ƙamari a yankin yayin da Isra’ila ta ƙaddamar da hare-haren sama a faɗin Iran, ciki har da sansanonin soji da na nukiliya, lamarin da ya sa Tehran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya.
Hukumomin Isra’ila sun ce aƙalla mutum 24 ne aka kashe yayin da ɗaruruwa suka ji rauni tun wancan lokacin a hare-haren makamai masu linzamin Iran.
Iran ta ce aƙalla mutum 224 ne aka kashe inda sama da mutum 1,000 suka ji rauni a harin Isra’ila.