Yanzu kwanaki 600 ke nan tun lokacin da Isra'ila ta fara yaƙinta a kan Gaza. Kwanaki 600 na hare-haren bama-bamai marasa tsayawa, yunwa da aka tsara, korar jama'a daga gidajensu, da kuma baƙin ciki mara misaltuwa.
Kuma duniya da ake kira mai wayewa ba tsayawa kallon lamarin ta yi ba kawai — ta taimaka wajen tabbatar da faruwar hakan kowace rana.
Me za ka kira kisan Falasdinawa fiye da 55,000, ciki har da yara sama da 16,000, amma Isra'ila ba ta fuskanci wani hukunci ba? Me za ku ce idan aka yi amfani da yunwa a matsayin makami?
Me za ku yi idan aka hana shigar da ruwa, man fetur, magunguna, da agajin jinƙai ga al'umma da mafi yawansu 'yan gudun hijira ne?
Za ku kira hakan kisan ƙare-dangi.
Wannan ba maganata ba ce kawai . Wannan kalma ce da manyan masana kisan ƙare-dangi, kungiyoyin kare hakkin bil'adama, da kuma wasu kwararrun Majalisar Dinkin Duniya, MDD suka yi amfani da ita.
A taƙaice ma, Jakada ta Musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Yankin Falasdinawa da aka mamaye, Francesca Albanese, ta bayyana cewa akwai “dalilai masu karfi na imani” cewa ana aikata kisan ƙare-dangi a Gaza.
Sanarwa ta hadin-gwiwa daga ƙwararru 20 na MDD ta yi gargadi game da “kisan ƙare- dangi da ke faruwa,” kuma wasu hukumomin MDD sun goyi bayan wannan ra'ayi.
Har ma wasu manyan jami'an agaji na MDD, kamar Mataimakin Sakatare-Janar Tom Fletcher, sun bayyana wannan kalma don bayyana abin da ke faruwa a Gaza.
Wannan ba kawai wata doka ba ce. Wannan kira ne na hankali.
Kuma yayin da hukumomin shari'a ke jan ƙafa wajen fahimtar abin da Falasdinawa suka daɗe suna ihu game da shi, ana ci gaba da jefa bama-bamai. Yara na cigaba da mutuwa.
Kuma gwamnatocin Ƙasashen Yamma na cigaba da ɗaukar nauyi da karewa, da kuma neman hujjar kare ƙasar da ke aikata kashe-kashen.
Na rubuta wannan ba kawai a matsayin Falasdinawa ba. Ba kawai a matsayin wanda ya rasa 'yan’uwa ba. Na rubuta a matsayin wanda ke kallon gazawar duniya a fili.
Dangina a Gaza har yanzu suna gudun hijira. Har yanzu suna fama da yunwa. Har yanzu suna cikin baƙin ciki. Har yanzu ba su da tsaro.
Na rubuta wannan maƙala daga London, inda na yi zanga-zanga, na yi kuka, na yi roƙo — yayin da gwamnatin Birtaniya ke cigaba da tattaunawa ko ayyukan Isra'ila suna kan daidai ko sun karya dokokin ƙasa da ƙasa.
A wani shirin siyasa na safiyar Lahadi, Mataimakiyar Firaminista ta Birtaniya, Angela Rayner, ta ce ba matsayinsu ba ne su tantance ko Isra'ila tana karya dokokin ƙasa da ƙasa.
Wannan, yayin da fiye da lauyoyi da alkalai 800 na Birtaniya suka sanya hannu a wata wasika zuwa ga Firaminista Keir Starmer, suna kira ga gwamnati ta dauki mataki a kan “munanan take hakkin ƙasa da ƙasa” da Isra'ila ke yi.
Kamar dai hankali wani zaɓi ne. Kamar dai matsayin Burtaniya ba shi ne dakatar da kashe-kashen ba, amma ci gaba da sayar da makaman da ke ba da damar faruwar hakan.
A wannan shirin, Kemi Badenoch — yanzu shugabar Jam'iyyar Conservative kuma mai yiwuwa Firaminista na gaba — ta tsaya a talabijin ta zargi Keir Starmer da “goyon bayan 'yan ta'adda.” Me yasa? Saboda ya amince cewa Isra'ila na iya aikata laifukan yaƙi.
Kwanaki 600 na kashe-kashe. Kuma har yanzu, tambayar da masu mulki suke yi kawai ita ce: “Amma Hamas fa?”
Kamar dai hakan ya halatta ƙona yara da ransu. Kamar dai hakan ya wanke kashe-kashen jama'a da yunwar da aka tsara ga al'umma gaba daya.
Bari in fada a fili: idan wannan ba kisan ƙare-dangi ba ne, mene ne?
A cikin wadannan kwanaki 600, Isra'ila ta kai harin bama-bamai a kan asibitoci, makarantu, masallatai, coci-coci, wuraren yin burodi, da sansanonin 'yan gudun hijira. Ta kashe duka iyalai — ta share sunayensu daga rajistar jama'a.
Ta kai hari a kan 'yan jarida, cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya, ma'aikatan agaji, da motocin daukar marasa lafiya. Ta ƙona mutane da ransu. Ta mayar da tantuna zuwa kaburbura.
Kuma duk tsawon wannan lokaci, shugabannin Ƙasashen Yamma sun mayar da martani da kalmomi marasa amfani, “damuwa” mara ma'ana, da gargadi marasa tasiri. Kamar dai Isra'ila na bukatar ƙarin gargadi. Kamar dai kashe-kashen yau da kullum ba gargadi ba ne da ya isa.
Lokacin da 'yar’uwata Juri mai shekaru shida ta mutu, tana barci a gadonta. Gidan danginmu — ba wani wuri a Gaza da za ka yi tunanin ya taba kasancewa mai cike da tsaro — an yi musu ruwan bama-bamai kuma aka rushe su.
'Yar’uwarta mai shekaru biyar ta ji rauni. Mahaifinta ya ji rauni.
Kakanta ma haka. An ciro gawar Juri daga cikin ɓaraguzao ta hannun 'yan’uwa kuma aka binne ta a kabari na jama'a — saboda akwai matattu da yawa a wannan rana da ba za a iya yi musu jana'iza yadda ya kamata ba.
Yaya za ka kare wannan? Yaya za ka wanke yunwar jarirai? Hare-haren da aka kai akan Rafah, inda aka ce iyalai su gudu “don tsira”? Kaburburan jama'a da aka gano kusa da asibitoci, inda aka ga alamun azabtarwa da kisan mutane?
Ba za ka iya ba — sai dai idan ka yi imani cewa rayukan Falasdinawa ba su da daraja.
Wannan shi ne tunanin da ba a fada ba a bayan kowace magana mara ma'ana, kowace sanarwa mai rauni na nuna “damuwa mai zurfi.”
Kisan da aka yi wa Isra'ilawa biyu a Washington DC a makon da ya gabata, ya zama babban labari a duniya.
Amma lokacin da aka kashe dubban yaran Falasdinawa, sai duniya ta tsaya tattauna ma'anar kisan ƙare-dangi — yayin da ake ci gaba da samar da makamai ga ƙasar da ke aikata kashe-kashen.
Wannan ba yaƙi ba ne tsakanin masu ƙarfi daidai. Bai taba zama haka ba. Wannan shi ne sojojin da suka fi ƙarfi a yankin — tare da goyon bayan ƙasashen da suka fi ƙarfi a duniya — suna kai hari a kan al'ummar da aka kulle a cikin wani yanki. Rabinsu yara ne.
Kuma duniya ba zura ido kawai ta yi hakan ke faruwa ba — ta taimaka wajen tabbatar da faruwar hakan.
Ba kawai ta hanyar yin komai ba. Amma ta hanyar yin abubuwa da yawa a hanyar da ba ta dace ba — hana mutane magana, korar 'yan jarida, haramta zanga-zanga, da kuma hukunta masu nuna goyon baya.
A Birtaniya, na ga mutane suna rasa ayyukansu kawai saboda sun ambaci kalmar “Falasɗinu.”
Na ga kafafen watsa labarai na Birtaniya suna ƙin amfani da kalmar “kisan ƙare-dangi” — yayin da suke ba da dama ga masu magana da ke goyon bayan Isra'ila wadanda ke musanta ma cewa yaran Falasdinawa suna wanzuwa.
Kwanaki ɗari shida.
Bai kamata ya dauki wannan lokaci ba. Kowace rana da yake cigaba ba kawai bala'i ba ne — zaɓi ne.
Kuma tarihi zai tuna cewa wannan kisan ƙare-dangi bai faru a ɓoye ba. Ya faru a fili. A cikin hotuna masu kyau. A kan kowace fuska. A kowace harshe.
Mun fada muku. Har yanzu muna fada muku.
Tambayar kawai yanzu ita ce: Za a dauki kwanaki nawa kafin duniya ta ce: haka ya isa?