AFIRKA
2 minti karatu
An ƙona miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Sefa biliyan 14 a Jihar Agadez ta Nijar
Ƙafar watsa labarai ta ActuNiger ta ba da rahoton cewa miyagun ƙwayoyin sun haɗa da tabar wiwi da ƙwayoyi masu sa maye irin su tiramadol da hodar ibilis da sauransu.
An ƙona miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Sefa biliyan 14 a Jihar Agadez ta Nijar
Dakarun tsaron Nijar sun ƙwato ƙwayoyin ne cikin watanni takwas da suka gabata / Actu Niger
2 Yuli 2025

An ƙona miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Sefa biliyan 14 ranar Talata a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar a wani mataki na yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ƙwayoyin, waɗanda rundunar tsaron Nijar ta ƙwace cikin watanni takwas da suka gabata, an ƙona su ne a ƙarƙashin jagorancin gwamnan yankin Manjo Janar Ibra Boulama Issa, a gaban mai gabatar da ƙara na babban kotun Agadez da kuma wasu jami’an fararen-hula da na soji.

Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa da misalin ƙarfe 11 na safiya ne aka cinna wuta kan tarin ƙwayoyin da suka kai ɗaruruwan kilogiram inda suka ƙone ƙurmus a wani lamarin da ke nuna matsa ƙaimin dakarun tsaron ƙasar a wannan muhimmim wurin ya da zango a yankin Sahel.

Ƙafar ta ba da rahoton cewa miyagun ƙwayoyin sun haɗa da tabar wiwi da ƙwayoyi masu sa maye irin su tiramadol da hodar ibilis da sauransu.

Baya ga yaba wa jami’an tsaro, hukumomi sun jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mutanen gari da jami’an tsaro a wani yanki inda yawan hamada yake bai wa masu fasa ƙaurin ƙwayoyi damar ɓuya a wurare da yawa.

Bikin ƙona ƙwayoyin wani mataki ne mai ƙwari wajen yaƙar sana’ar ta laifi a tsakiyar hamadar Sahara inda Agadez ya kasance wani wurin ya da zango.

A matsayinsa na wajen ya da zango da wurin haƙar zinari da kuma hanyar wucewa arewa, yankin Agadez na fama da matsaloli na tsaro. Hukumomin Nijar na son ci gaba da sanya ido a ko da yaushe domin hana  yankin ya zama wata cibiyar aikata laifuka na ƙasa da ƙasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us