GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Sojan Isra'ila ya kashe kansa saboda firgicin da ya shiga a yaƙin Gaza
Sakamakon yawan mafarkin gawawwaki da rashin sukuni saboda jin “warin mutuwa” da tsananin firgici da Daniel Adri mai shekara 24 ya shiga, hakan ya sa ya tafi daji ya kashe kansa bayan ya kasa gano yadda zai magance damuwar da yake ciki.
Sojan Isra'ila ya kashe kansa saboda firgicin da ya shiga a yaƙin Gaza
A watan Mayu, jaridar Haaretz ta Isra'ila ta ce sojoji 42 sun kashe kansu tun bayan ɓarkewar yakin Gaza. / REUTERS
7 Yuli 2025

Wani sojan ko-ta-kwana na Isra’ila ya kashe kansa sakamakon tsananin firgici da damuwar da ya shiga a yaƙin Gaza wanda Isra’ila ke aikata kisan-kiyashi.

Shafin labarai na Isra'ila, Walla, ya bayyana cewa Daniel Adri, mai shekaru 24, wanda ya yi aiki a Gaza da Lebanon, ya kashe kansa bayan doguwar gwagwarmayar da ya yi da matsaloli masu alaƙa da damuwa da kuma rasa abokai biyu a yaƙin na Gaza.

An gano gawar sojan a cikin wani daji kusa da birnin Safed a arewacin Isra'ila bayan ya kasa samun sukuni da yadda zai yi ya magance damuwar da ya shiga.

"Ba zai iya jurewa ba kuma ya koka da ganin hotunan gawawwaki da kuma jin warin mutuwa a kullum," in ji mahaifiyarsa.

Yawaitar kashe kai daga sojojin Isra’ila

A cewar kafafen yaɗa labarai na Isra'ila, adadin sojojin da suka kashe kansu ya ƙaru tun bayan ɓarkewar yakin Gaza a watan Oktoban 2023.

Wani rahoto daga jaridar Israel Hayom ya nuna cewa sojoji 21 sun kashe kansu a shekarar 2024.

A watan Mayu, jaridar Haaretz ta Isra'ila ta ce sojoji 42 sun kashe kansu tun bayan ɓarkewar yakin Gaza.

Duk da kiran duniya na tsagaita wuta, Isra'ila ta ci gaba da aikata kisan ƙare-dangi a Gaza, inda ta kashe fiye da mutum 57,400, yawancinsu mata da yara, tun daga watan Oktoban 2023.

Takardun kama Netanyahu daga ICC

A watan Nuwambar bara, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta fitar da takardun kama a Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaronsa Yoav Gallant saboda laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.

Haka kuma Isra'ila tana fuskantar shari'ar kisan ƙare-dangi a Kotun Duniya saboda yaƙin da take yi a Gaza.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us