Ministan yawon buɗe ido na Kamaru, Bello Bouba Maigari, ya amince da tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen da ake sa ran za a gudanar a watan Oktoba, duk da cewa Shugaba Paul Biya wanda ya shafe tsawon shekaru kan mulki bai bayyana ko zai sake tsayawa takara ba.
Maigari, wanda tsohon Firaiminista ne kuma mai shekaru 78, ya kasance babban abokin Shugaba Biya na tsawon fiye da shekara 30.
Ya karɓi takarar jam’iyyar National Union for Democracy and Progress (NUDP) a ranar Asabar, duk da cewa bai yi murabus daga mukaminsa na majalisar ministoci ba.
Shi ne minista na biyu daga arewacin Kamaru da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 'yan kwanakin nan, abin da ke nuna yiyuwar samun rarrabuwar kawuna tsakanin gwamnatin tsakiya ta Biya da manyan shugabannin arewa masu tasiri.
Babu ƙarin bayani kan takarar Biya
Tun daga shekarar 1982, Biya ya kasance shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya mai shekaru 92. Har yanzu bai tabbatar ko zai sake tsayawa takara ba.
Sanarwar Maigari ta biyo bayan murabus din wani ɗan arewa, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya kasance tsohon mai magana da yawun gwamnati.
A makon da ya gabata, Bakary ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara, yana mai cewa akwai kira mai yawa daga jama’a na neman sauyi.
Jihohin arewacin Kamaru guda uku – Adamawa, Arewa da Arewa Mai Nisa – suna da masu jefa ƙuri’a fiye da miliyan biyu, abin da ke ba su tasiri mai yawa a zaɓen.
Fiye da ‘yan Kamaru miliyan takwas sun yi rajistar zaɓe, a cewar bayanan wucin-gadi daga hukumar zaɓe a wannan ƙasa mai arzikin koko da man fetur da ke tsakiyar Afirka wadda ke da yawan jama’a kusan miliyan 30.