AFIRKA
2 minti karatu
Shiga tsakani na gaggawa ya dawo da zaman lafiya a babban birnin Libiya bayan jerin sabbin arangama
An dawo da zaman lafiya babban birnin Libiya Tripoli bayan sabbin jerin arangama tsakanin ƙungiyoyi masu makamai a ranar Litinin.
Shiga tsakani na gaggawa ya dawo da zaman lafiya a babban birnin Libiya bayan jerin sabbin arangama
FILE PHOTO: Members of the 444 Brigade of the Libyan Army stand guard at Abu Salim area in Tripoli / Reuters
9 Yuni 2025

An dawo da zaman lafiya a babban birnin Libiya Tripoli bayan sabbin jerin arangama tsakanin ƙungiyoyi masu makamai ranar Litinin sakamakon matakin da Kwamitin Sulhu da shugaban ƙasar ya kafa ya ɗauka.

Emced el-Malti, Kwamandan Rundunar ko ta Kwana ta 222 kuma ɗaya daga cikin ‘yan kwamitin sulhu, ya shaida wa kafafan watsa labarai cewa kwanciyar hankali ya dawo a babban birnin bayan sa hannun “dakarun warware rikicin”.

Malti ya bayyana cewa dakarun na “warware rikici” an tura su dukkan wuraren da ake rikici a sassan Tripoli.

Abubuwan da suka auku a Tripoli

Jerin arangama sun ɓarke a babban birnin ƙasar bayan an kashe shugaban wata ƙungiyar ‘yan bindiga a Tripoli mai suna Stability Support Unit, a ranar 12 ga watan Mayu.

Gwamnati ta bayyana hakan a wata sanarwa jim kaɗan bayan runduna ta 444, da ke da alaƙa da ma’aikatar tsaro ta karɓe iko da hedikwatar Stability Support Unit da kewayensa a unguwar Abu Salim a birnin Tripoli.

A wata sanarwa ranar 13 ga watan Mayu, Firayiminista Abdulhamid Dibeybe, ya taya sojoji da ‘yan sanda murnar nasarar da suka yi wajen tabbatar da ikon ƙasar cikin lamuran da suka auku a Tripoli.

Wasu jerin arangama sun ɓarke tsakanin dakarun gwamnati da da kuma ‘yan ƙungiyar “Rada,” wata ƙungiyar ‘yan bindiga mai ƙarfi a babban birnin ƙasar, cikin sanyin safiyar ranar 14 ga watan Mayu, kuma an ga hayaƙi na tashi daga wasu gidaje a sassan birnin na Tripoli.

Da misalin ƙarfe 12 na rana, Ma’aikatar Tsaron Libiya ta bayyana tsagaita wuta a dukkan sassan Tripoli domin kare fararen hula.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us