AFIRKA
2 minti karatu
Senegal ta haramta amfani da babura a kusa da iyakarta da Mali
Dokar hana amfani da baburan wadda za ta rinƙa aiki daga tsakar dare zuwa wayewar gari ta shafi yankin Bakel na Senegal, wanda ke da tsayin kilomita 230 a kan iyaka da Mali.
Senegal ta haramta amfani da babura a kusa da iyakarta da Mali
Mali na fama da rikicin tsaro da tashin hankali daga ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Daesh fiye da shekara goma. / Getty
26 Yuli 2025

Hukumomin Senegal sun saka dokar hana zirga-zirgar babura da daddare a wani yanki na gabashin ƙasar, bayan da 'yan ta'adda suka yi amfani da baburan wajen kai hare-hare a wasu garuruwa da ke iyaka da Mali.

Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne “saboda dalilai na tsaro,” bayan da maharan suka kai farmaki kan sansanonin sojoji a wasu garuruwan Mali a ranar 1 ga Yuli, inda aka kashe aƙalla farar hula guda.

Ɗaya daga cikin garuruwan Mali da aka kai wa hari, Diboli, na da tazarar ƙasa da mita 500 ne kacal da Kidira a Senegal.

Dokar hana amfani da baburan wadda za ta rinƙa aiki daga tsakar dare zuwa wayewar gari ta shafi yankin Bakel na Senegal, wanda ke da tsayin kilomita 230 a kan iyaka da Mali.

Kungiyar 'yan ta'adda ta JNIM, mai alaka da Al-Qaeda, wadda ke aiki a Mali, Nijar da Burkina Faso, ce ta ɗauki alhakin hare-haren da suka faru a ranar 1 ga Yuli.

Da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntubi gwamnatin yankin Bakel a ranar Asabar, sun ƙi yin tsokaci kan dokar da aka kafa.

Mali na fama da rikicin tsaro da tashin hankali daga ƙungiyoyin da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Daesh fiye da shekara goma.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us