KIMIYYA DA FASAHA
1 minti karatu
Ayyukan mata na fuskantar barazanar AI fiye da na maza- Rahoton MDD
Rahoton Kungiyar Kwadago ta Duniya ya gano cewa za a sake fasalin kashi 9.6 cikin 100 na ayyukan da mata ke yi da na ƙirkirarriyar basira AI, idan aka kwatanta da kashi 3.5 na da ake da su a bangaren maza.
Ayyukan mata na fuskantar barazanar AI fiye da na maza- Rahoton MDD
Ayyukan mata na fuskantar barazanar AI fiye da na maza- MDD/ AP
21 Mayu 2025

Ayyukan da mata suka fi yi sun fi fuskantar barazanar sauya su da ƙirkirarriya basira fiye da wadanda maza ke yi, musamman a ƙasashe masu tasowa, in ji rahoton kungiyar kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton ya gano cewa, ana shirin sake fasalin kashi 9.6 na ayyukan da aka fi sanin mata na yinsu idan aka kwatanta da kashi 3.5 na waɗanda maza ke yi da na ƙirkirrariyar basira ta AI wadda ke ƙara ɗaukar ayyukan da ake gudanarwa da koyarwa kamar aikin sakatariya.

Ko da yake za a buƙaci gudumawar ɗan adam a ayyuka da dama - kuma akwai yiwuwar a sauya su maimakon kawar da su baki daya, in ji rahoton a ranar Talata.

Ayyuka a kafofin watsa labarai, da na tsare-tsaren software da ayyukan da suka danganci kuɗi suma suna kan gaba wajen fuskantar wannan sauyi yayin da AI ke dada haɓaka iliminsa.

"Muna jaddada cewa irin wannan tsarin ba ya nufin sarrafa kai tsaye na gabaɗayan sana'a ba, a'a, yuwuwar samun babban kaso na ayyukanta na yanzu da za a yi ta amfani da wannan fasaha," in ji rahoton.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us