AFIRKA
2 minti karatu
ECOWAS 'tana da ƙwarin gwiwar' cewa Burkina Faso, Mali da Nijar za su koma cikin kungiyar
Ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka ta ce, tana da ƙarin gwiwar cewa Burkina Faso da Mali da Nijar za su koma cikinta bayan ficewarsu a Janairun 2025.
ECOWAS 'tana da ƙwarin gwiwar' cewa Burkina Faso, Mali da Nijar za su koma cikin kungiyar
West African regional bloc ECOWAS says efforts are under way to return Burkina Faso, Mali and Niger to the bloc. / TRT Afrika Français
28 Mayu 2025

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) tana da “yakinin” cewa Mali, Burkina Faso da Nijar za su dawo cikin kungiyar, in ji Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, a ranar Laraba.

“An yi magana sosai kan ficewar wasu daga cikin kasashenmu uku, har ta kai ga an kau da hankali daga manyan nasarorin da al’ummarmu ta samu. Amma dimokuradiyya tsari ce, ba wani abu daya ba,” in ji Tuggar a bikin cika shekaru 50 na ECOWAS da aka gudanar a Nijeriya.

Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya bayyana farin cikinsa cewa “ko da ba tare da ‘yan’uwanmu da suka bar kungiyarmu ba,” Ƙungiyar Yammacin Afirka tana da “fahimtar bukatar ci gaba tare a matsayin iyalin Yammacin Afirka.”

Mali, Burkina Faso da Nijar – wadanda suka kafa Kungiyar Jihohin Sahel (AES) – sun sanar da niyyarsu ta ficewa daga ECOWAS a ranar 29 ga Janairu, 2025, suna mai bayyana rashin jin dadinsu kan takunkumai da kuma zargin tasirin kasashen waje, bayan juyin mulki a kasashen Sahel uku.

A hukumance, kasashen uku sun fice daga ECOWAS a ranar 29 ga Janairun 2025, inda suka bar kungiyar da mambobi 12 kacal. ECOWAS ta tsara wa’adin watanni shida daga 29 ga Janairun 2025, zuwa 29 ga Yulin 2025, domin karfafa AES su sake tunani kan ficewar.

Kungiyar AES ta kafa yarjejeniyar tsaro ta hadin-gwiwa a watan Satumba 2023, wadda aka tabbatar da ita a matsayin tarayya a ranar 6 ga Yuli, 2024, tare da sanya hannu kan wata yarjejeniya don zurfafa hadin kai a bangarorin tsaro, tattalin arziki da zamantakewa.

Gwamnatocin da sojoji ke jagoranta sun dauki matakai masu karfi don sake tsara dangantakarsu ta kasa da kasa, ciki har da ficewa daga ECOWAS da Kungiyar Kasashen Faransanci (OIF).

Haka kuma, AES ta sanar da shirin tura rundunar hadin gwiwa mai dauke da sojoji 5,000 domin yakar barazanar ta’addanci da ke kara yawaita a yankin.

Karin shirye-shirye sun hada da kaddamar da fasfo na bai-ɗaya da kuma tashar talabijin ta yanar gizo domin yakar yada bayanan karya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us