Cutar kwalara ta barke a babban birnin kasar Sudan inda ta kashe mutane 70 cikin kwanaki biyu, a cewar jami’an kiwon lafiya, annobar dai na ci gaba da yaduwa cikin sauri a durkushershiyar yanayin kiwon lafiya da kasar ke fama da shi.
Ma'aikatar lafiya ta jihar Khartoum a ranar Alhamis a cikin sanarwar da ta fitar ta ce, ta sami sabbin mutane 942 da suka kamu da cutar, yayin da 25 suka mutu a ranar Laraba, bayan jimillar mutane 1,177 sun kamu da cutar kana 45 suka mutu a ranar Talata.
Sojojin Sudan sun zargi dakarun Rapid Support Forces (RSF) da kaddamar da hare-hare a gabaki ɗaya fadin birnin Khartoum a farkon wannan wata, ciki har da tashohin wutar lantarki guda uku, lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki da ruwan sha tare da barkewar cutar kwalara.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, ma'aikatar lafiya ta ba da rahoton mutane fiye 2,700 da suka kamu da cutar kwalara, yayin da daga ciki 172 suka mutu a cikin kwanaki bakwai kacal a jihohi shida, inda kashi 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar suka fito daga a jihar Khartoum.
Mumunan yaki
Cutar kwalara na yaduwa a kasar Sudan, sai dai yawan barkewar cutar da yawaitarta na kara muni tun bayan barkewar yakin a shekarar 2023, inda ya yi sanadin lalata hanyoyin ruwa, da tsaftar muhalli da kuma kayayyakin kiwon lafiya.
A ranar Talata, ma’aikatar ta ce mutane 51 daga cikin 2,300 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, kana kashi 90 cikin 100 na rahotoni bullar cutar da aka samu a cikin makonni uku da suka gabata sun fito ne daga jihar Khartoum.
Ƙungiyar likitocin Sudan ta yi gargadin cewa, alkaluman da ke kasa sun zarce yawan adadin da ma'aikatar ta bayar, inda daruruwan mutane suka mutu a babban birnin kasar kadai.
Kazalika a wata sanarwa da ta fitar, ungiyar ta yi gargadin cewa akwai “karancin allura, da kuma karancin hanyoyin ruwa mai tsafta da kuma rashin kayayyakin aiki na mata masu juna biyu da ke kashe kwayoyin cuta” in ji asibitocin birnin.