Hukumar Lafiya ta Ghana (GHS) ta sanar da ƙarin mutane 14 da suka kamu da cutar kyandar biri (Mpox), yayin da adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a ƙasar ya kai 133.
A wata sabuwar sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ya zuwa ranar 26 ga watan Yuni ba a samu rahoton mutuwa ko kwantar da wani a asibiti ba, amma an gano waɗanda suka kamu da cutar a gundumomi 46 a yankuna 10.
A cewar hukumar ta GHS, an gano cutar Mpox a gundumomi 16 a yankin Greater Accra, da gundumomi 10 a yankin Yamma, sai biyar a yankin Arewa ta Yamma, hudu a tsakiya, uku-uku a yankunan Ashanti da Volta da dai sauransu.
Hukumar ta GHS ta ce tana ci gaba da sa ido a faɗin yankuna 16 a kasar ta hanyar tsarin sa-idonta na musamman.
Kazalika GHS ta ƙara da cewa, shugabannin hukumomin lafiya na yankin sun ɗauki matakan kula da lafiyar jama'a, gami da bibiyar waɗanda suka yi mu’amala da masu ɗauke da cutar don taimakawa wajen daƙile yaduwar cutar.
A farkon watan Yuni ne Darakta-Janar na GHS, Farfesa Samuel Kaba Akoriyea, ya bayyana cewa babu wata barazana ta yaɗuwar cutar yana mai kwantar wa jama’a hankula.
Ya jaddada cewa tsarin kiwon lafiyar jama'a na Ghana yana cikin shirin ko-ta-kwana kuma ana bin ka'idojin ɗaukar matakai da taƙaita duk wata cuta da ake iya kamuwa da ita.
Yaɗuwar Mpox
Mpox cuta ce da ke yaɗuwa tsakanin mutanen da suka yi cuɗanya da juna, kuma tana da alamomi masu kama da na mura da ƙuraje da zazzabi da ciwon kai da jiki da baya da yawan kasala da gajiya da kuma kumburi na wasu sassan jiki.
Hukumar GHS ta shawarci jama'a da su tsaftace muhallinsu, kana su guji kusanci da mutanen da suka nuna alamun cututtuka masu yaduwa, da kuma kai rahoton duk wani wanda ake zargi da cutar da sauri zuwa wuraren kiwon lafiya.
"Muna da kwarewa da kuma kayan aiki da za mu iya taƙaita wannan lamarin da kuma hana ɓarkewar wata babbar annoba," in ji GHS, tana mai jaddada kudirin gwamnati na kiyaye lafiyar jama'a.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana Mpox a matsayin cuta mai matuƙar haɗari ga jama’a a watan Agustan 2024, bayan yaduwar wani sabon nau’in cutar a nahiyar Afirka.
Tun daga wannan lokacin, sama da kasashen Afirka 13 ne aka samu rahoton bullar cutar a cikinsu, kana Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka CDC ta tattara rahoton fiye da mutum 17,000 da ake zargin sun kamu da cutar da kuma mutuwar 517 a shekarar 2023.
WHO ta amince da rigakafin farko na MPox a bara don inganta hanyoyin kariya ga al'ummomin da ke cikin barazanar hadarin cutar a fadin nahiyar, inda sama da mutane 20,000 suka kamu da cutar.