AFIRKA
2 minti karatu
Boko Haram: An kashe mutane da dama a arewa maso-gabashin Nijeriya
Hare-Haren na karshen mako, da suka yi ajalin mutane 22, sun zo ne a lokacin da yankin ke sake shaida dawowar hare-haren ‘yan ta’adda.
Boko Haram: An kashe mutane da dama a arewa maso-gabashin Nijeriya
Wata mace na wuce wa ta shingen binciken ababan hawa na sojoji a Gwoza, Jihar Borno. / AP
28 Afrilu 2025

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kashe a kalla mutane 22 tare da jikkata wasu da dama a hare-hare biyu daban-daban da suka kai a arewa maso-gabashin Nijeriya, in ji jama’ar yankin da ‘yan sanda.

Nijeriya na fama da ta’addanci na tsawon lokaci a iyakokinta na arewa maso-gabas, inda ‘yan ta’addar Boko Haram ke kai hare-hare tare da reshenta na ISWAP da ya ɓalle.

A jihar Adamawa, wasu da ake zargin ‘yan ta’addar Boko Haram ne sun kashe mutane 10 da jikkata wasu da dama a harin da suka kai wa kauyen Kopre, shi ma a ranar Asabar, in ji mazauna yankin.

Hare-Haren sun nufi mafarauta da fararen hula da suka tashi don kare yankunansu. ‘Yan sanda sun kai karin jami’ai Kopre, wanda ke yankin Hong na jihar Adamawa, in ji kakakin ‘yan sanda Suleiman Yahaya Nguroje a ranar Litinin.

A Jihar Borno, wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne sun kai harin kwantan bauna tare da kashe fareren hula 10 da jami’an tsaro biyu a ranar Asabar, in ji Mohammed Shehu Timta, sarkin yankin Gwoza da ke Borno. Wasu mutanen biyu kuma sun samu raunuka.

A farkon wannan watan, gwamnan Borno ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram sun sabunta hare-hare da garkuwa da mutane, suna taɓarbara yanayin tsaron da aka samu a yankin.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us